1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben raba gardama a Zimbabwe

March 15, 2013

Shugaba Robert Mugabe na ganin daftarin sabon kundin tsarin mulki, a matsayin wata nasara da gwamnatinsa ta cimma kan makomar demokradiyyar Kasar.

https://p.dw.com/p/17ybW
Zimbabwean President Robert Mugabe, gestures, during the country's Heroes Day Commemorations, in Harare, Monday, Aug. 13, 2012. Zimbabwe's president says his party's symbol of a raised fist was used to fight colonial-era white rule and is not a gesture of violence toward fellow Zimbabweans. President Robert Mugabe said Monday that the power of the fist symbol helped the party defeat colonial oppression and urged the nation to prepare peacefully for a referendum on a new constitution and elections afterward. (Foto:Tsvangirayi Mukwazhi/AP/dapd)
Hoto: AP

A kan bayyana shugaba Robert Mugabe mai shekaru 89 da haihuwa da kasancewa daya daga cikin shugabannin nan na sai madi ka ture, wanda ke rayuwa cikin daula duk kuwa da matsanancin mawuyacin hali da Zimbabwe ke ciki sakamakon durkushewar tattalin arziki. Al'ummarta dai na ci gaba kasancewa cikin talauci, a yayin da babu komai a baitul malin gwamnatin wannan kasa da ke da dumbin albarkatun kasa na lu'u lu'u, wadda kuma ba za ta iya daukar nauyin gudanar zaben raba gardamar karshen mako, ba tare da tallafi daga ketare ba.

Shugaba Mugabe ya shaida wa magoya bayan jam'iyyarsa ta Zanu-PF, daftarin kundin tsarin mulkin wani sabon babi ne:

Ya ce "bari fadi wani abu game da daftarin kundin tsarin mulkin. Babu wani abu mummuna tare da shi, ko kadan babu. Akwai 'yan abubuwan da zamu iya yin gyara akansu nan gaba. Amma yanzu bari mu bada kuri'unmu da murya guda, mu lashe zaben. Babu shakka zamu lashe zaben"

Zimbabwe's Prime Minister Morgan Tsvangirai addresses a meeting with representatives of civic groups in Harare on February 13, 2013 where he announced announced that the country will hold a constitutional referendum in March followed by elections in July, a timetable that will decide the fate of veteran President Robert Mugabe. Zimbabweans will be asked to vote on a basic law that would, for the first time, set presidential term limits and abolish the head of state's immunity. AFP PHOTO / Jekesai Njikizana. (Photo credit should read JEKESAI NJIKIZANA/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Shima Prime minista Morgan Tsvangirai dake gwamnatin hadaka da Mugabe tare da jam'iyyarsa ta MDC, suna goyon bayan daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar. Bayan zaben shekara ta 2008, an yi dauki ba dadi da ya haddasa zubar da jini tsakanin magoya bayan jam'iyyun biyu. A zahirance dai gwamnatin hadakar ta jeka na yi ka ce tsakanin Mugabe da Tsvangirai. Gyaran kundin tsarin mulkin kasar dai ya kasance babban muradin kasashen duniya.

A yanzu haka dai tsoron barkewar sabon rikici na barazana ga zaben kuri'ar raba gardamar akan kundin tsarin mulkin da ya dauki shekaru uku ana aiki akansa, kuma mai shafuna 150. A farkon watan Fabrairu ne dai aka kammalashi, abunda za'a iya cewar babu isasshen lokaci wa masu zabe su yi nazarinsa kafin kada kuri'un nasu.

Abun da ke kunshe a Kundin

Yvonne Mashayamombe daliba ce da ta kammala jami'a, kuma ke shirin kada kuri'arta a zaben na karshen mako.

Ta ce " akwai damarmaki masu yawa wa mata a wannan daftarin kundin tsarin mulkin. Hukumar kula da daidaita jinsi da aka sanya a ciki, zata tabbatar da cewar an bawa mata 'yancinsu, wanda ke nuna irin damar da suke da ita na kyakkyawar wakilci a kowane mataki".

Sabon daftarin kundin tsarin mulkin dai ya yiwa mata tanadin kujeru 60 zuwa 150 a majasar wakilan kasar.

Zimbabweans wait in line 09 March 2002 to vote at a polling station in the Mbare shantytown of Harare at the start of two days of voting for the presidential elections. Zimbabweans started voting 09 March 2002 in an election pitting President Robert Mugabe against opposition leader Morgan Tsvangirai. dpa
Hoto: picturr

Muhimman sauye sauyen dake kunshe cikin daftarin kundin dai shine rage ikon shugaban kasa, tare da takaita madafan ikonsa akan 'yansanda da soji, kuma rage kariyar da yake da ita. Sai kuma wa'adin mulki na shekaru biyar biyar sau biyu ga kowane shugaba, amma ba za'ayi la'akari da wanda ya gabata ba, ma'ana yanzu ne za'a fara amfani da wannan tsarin , wanda ke nuni da cewar shugaba Robert Mugabe zai iya ci gaba da mulki har zuwa lokacin da zai cika shekarun 99.

Matsayin Kungiyoyi masu zaman kansu

Lovemore Madhuku mai fafutukar kare hakkin jama'a ne kuma shine shugaban majalisar kundin tsarin mulki mai zaman kanta da ake kira NCA. Ya dauki tsawon shekaru 15 yana fafutukar ganin an samar da sabon kundin tsarin mulki, tare da adawa da karfin ikon shugaban kasa.

Ya ce " ba sirri bane, cewar gazawar Mugabe wajen jagorantar kasarmu kamar yadda ya kamata, ba zai kasa nasaba da cewar babu wanda ya isa ya kalubalance shi ba, domin shine ke da karfin iko akan komai".

A ra'ayin Madhuku dai matsalar ba zata sauya zane ba koda a wannan daftarin sabon kundin tsarin mulkin. Dangane da haka yayi kira ga sauran kungiyoyin fafutukar kare hakkin bil Adama da su kauracewa zaben na ranar Asabar 16 ga watan Maris.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi