1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben rabin wa'adin na Amirka

Suleiman Babayo
November 8, 2018

An samu gagarumin fitowa a zaben rabin wa'adi na Amirka inda jam'iyyar Democrats ta lashe zaben majalisar wakilan Amirka inda Republican mai mulki ke da rinjaye a majalisar dattawa.

https://p.dw.com/p/37u7w
Nancy Pelosi
Hoto: Reuters/J. Ernst

Zaben tsakiyar wa'adi a Amirka ya nunar da cewa jam'iyyar Democrats ke da rinjaye a zaben 'yan majalisar wakilai bayan samun kujeru sama da 220 daga cikin kujeru 435. Ita kuwa jam'iyyar Republican mai mulkin Amirka ke da rinjaye a majalisar dattawan kasar da kujeru sama da 50 daga cikin dari, kafin sakamako na karshe, matakin da ka iya jawo sauyin lamura a siyasar Shugaba Donald Trump.