1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Girka

December 23, 2014

A wannan Talata ce 'yan majalisun dokokin a Girka ke kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, inda ake shakkun fadawar kasar cikin wani rikici na siyasa.

https://p.dw.com/p/1E91B
Hoto: Reuters/Alkis Konstantinidis

Firaministan kasar Antonis Samaras, wanda wa'adin mulkinsa ke karewa a tsakiyar shekara ta 2016, ya ce a shirye yake ya sanya 'yan majalisu masu akidar Turai cikin gwamnatinsa idan har suka zabi dan takararsa Stavros Dimas, tare da alwashin shirya zaben 'yan majalisun daga shekara mai zuwa ta 2015. Sai dai ana ganin akwai wuya Firaministan ya iya samun rinjaye na kuri'un 'yan majalisu 200 wadanda za su ba da damar zaben dan takararsa, ganin yadda a zagaye na farko ya samu kuri'u 160 daga cikin kuri'un 'yan majalisun 300 da ke wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo