1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Tunusiya: Nidaa Tounis na kan gaba

November 25, 2014

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Tunusiya ta ce 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasar kasar guda biyu ne za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1Dssf

Wannan dai ya biyo bayan gaza lashe kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar da ya gabata da duka 'yan takarar suka yi. Sakamakon zaben ya nunar da cewa dan takarar shugabancin kasar daga jam'iyyar Nidaa Tuonis Beji Caid Essebsi ne ke kan gaba da kaso 39 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da shugaban kasar mai ci yanzu kuma tsohon mai rajin kare hakkin dan Adam na jam'iyyar Ennahda Moncef Marzouk ya samu kaso 33 cikin 100 na kuri'un. A yanzu dai 'yan takarar biyu za su yi zawarcin magoya bayan sauran 'yan takarar da basu tabuka rawar azo a gani ba a zaben, musamman ma Hamma Hammami dan takarar da ya zo na uku da kusan kaso takwas cikin dari na kuri'un da aka kada. A watan Disamba mai kamawa ne dai ake sa ran gudanar da zagaye na biyu na zaben kasar ta Tunusiya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal