1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Zimbabwe ya gudana ba tare da babbar matsala ba

July 31, 2013

Duk da fargabar tafka magudi da 'yan adawa suka yi a Zimbabwe, masu sanya ido sun nuna gamsuwa da yanayin zaben.

https://p.dw.com/p/19HwJ
Zimbabweans line up near a polling station in Harare to vote in a general election on July 31, 2013. Zimbabwe was readying for an inadequately prepared yet tight election battle that could see President Robert Mugabe extend his 33-year grip on power. From a list of five candidates, voters will chose who will lead the nation for the next five years after a compromise government forced by a crisis ignited by the 2008 presidential run off. But the real battle is between Mugabe and his perennial rival Prime Minister Morgan Tsvangirai AFP/PHOTO Jekesai Njikizana. (Photo credit should read ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images)
Hoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Hukumar zaben Zimbabwe ta bayyana fatan fara sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana, wanda zai kawo karshen gwamnatin kawancen da ta mulki kasar na tsawon shekaru hudu. Sai dai ko da shike babbar jam'iyyar adawar kasar ta MDC ta bayyana fargabar tafka magudi, amma rahotanni sun nunar da cewar ba a samu manyan matsaloli ba.

Duk da cewar zargin tafka magudi daga babban abokin hamayyar shugaba Mugabe, wato firaministan kasar Morgan Tsvangirai ne ya mamaye shirin zaben, amma masu sanya ido a kan zaben na wannan Larabar da kuma ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya suka ce babu wasu manyan matsaloli a yanda zaben ya gudana, kuma hatta shi kansa Morgan Tsvangirai bayyana gamsuwarsa ne yayi da zaben da ya ce yana ciki da tarihi, bayan kada kuri'arsa da safe:

Ya ce " Wani lokaci yanayi ne mai sosa rai idan ka ga wadannan dimbin mutane. Bayan tsoratarwa, da rigingimun da aka samu, da saiko da rashin yarda da juna da kuma bita da kulli, a karshe dai, an sami yanayi na zaman lafiyar da za a iya cewar Zimbabwe za ta sake komawa bisa turbar ci gaba."

Zimbabwe's President Robert Mugabe casts his vote as his wife Grace and daughter Bona (L-R) look on in Highfields outside Harare July 31, 2013. Zimbabweans voted in large numbers on Wednesday in a fiercely contested election pitting veteran President Robert Mugabe against Prime Minister Morgan Tsvangirai, who has vowed to push Africa's oldest leader into retirement after 33 years in power. With no reliable opinion polls, it is hard to say whether 61-year-old Tsvangirai will succeed in his third attempt to unseat 89-year-old Mugabe, who has run the southern African nation since independence from Britain in 1980. REUTERS/Siphiwe Sibeko (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS TPX IMAGES OF THE DAY)
Shugaba Mugabe yayin jefa kuri'aHoto: Reuters

Shirin farfado da tattalin arzikin Zimbabwe

Shi ma kansa shugaba Mugabe, wanda shekarunsa na haihuwa 89 ne, bayyana shirye shiryen sake farfado da tattalin arzikin Zimbabwe ne yayi bayan jefa kuri'ar ta sa. Sai da dai a yayin da yake amsa tambayar ko zai iya kaiwa karshen wa'adin mulkinsa dubi da cewar, zai kai shekaru 94 ne a lokacin. Ga amsar da ya bayar:

"Ko zan kammala? Me zai hana? Ko dai ba ka son in kammala ne? Me yasa aka zabe ni. Me ma zai sa in tsaya takara, in har daga baya zan yi murabus?"

Shugaba Robert Mugabe dai bai kyale masu sanya ido na kasashen yammacin duniya lura da zaben kasarsa ba, domin kuwa a cewarsa, ba sa kaunarsa, saboda haka ba za su yi adalci a irin abubuwan da za su fada dangane da zaben ba. Sai dai kuma akwai masu sanya ido daga ketare, kamar dai tawagar kungiyar ci gaban kasashen kudancin Afirka, wadda aka fi sani da suna SADC. Ibrahim Ibrahim, mukaddashin ministan kula da harkokin wajen Afirka Ta Kudu, daya ne daga cikin 'yan tawagar:

Ya ce " Ya zuwa yanzu dai, babu tsoratarwa ko wani rikici ko kuma wata takala, amma dai ya zuwa yanzu aikin jefa kuri'ar na tafiya yanda ya dace. Sai dai kuma ba zamu yi gaggawar yanke hukunci ba, domin bamu san yanda lamarin yake ba a sauran sassa na kasar, amma dai anan birnin Harare, na lura da cewar komi na tafiya salum-alum."

Zimbabwean opposition Movement For Democratic Change (MDC) leader Morgan Tsvangirai (L) casts his vote with his wife Elizabeth in Harare, July 31, 2013. Zimbabweans voted on Wednesday in a fiercely contested election pitting President Robert Mugabe against Tsvangirai, who has vowed to push Africa's oldest leader into retirement after 33 years in power. REUTERS/Philimon Bulawayo (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Tsvangirai yana ka'da kuri'aHoto: Reuters

Makomar gwamnatin kawance

Sai dai kuma hatta a ranar zaben ma, jam'iyyar MDC na ci gaba da zargin cewar, hukumar zaben Zimbabwe na kokarin tafka magudi domin ganin cewar jam'iyyar ZANU - PF ta shugaba Mugabe ne ta yi nasara.

A dai daya daga cikin runfunan zabe, wasu 'yan kasar suka ce, a yayin da suka isa an sanya alamar sun jefa kuri'a akan sunayesu, duk da rashin yin zaben. Sai dai a lokacin da mataimakiyar shugabar hukumar zaben ke mayar da martani akan hakan, cewa ta yi za su binciki dukkan zarge-zarge da nufin daukar matakin da ya dace.

Dama zargin tafka magudin ne, da rikicin da ya biyo bayansa, yasa shugaba Mugabe kafa gwamnatin kawance tare da Morgan Tsvangirai a matsayin firaminista a shekara ta 2008, inda kuma suka yi abinda wasu ke cewar ya yi kama da zaman doya da manja ne na tsawon shekaru hudu, kawancen da kuma ake ganin sakamakon wannan zaben, zai kawo karshensa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani