1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafin rana ya hallaka mutane da dama a Indiya

Salissou BoukariMay 25, 2015

Fiye da mutane 430 ne suka rasu a wasu yankunan kasar Indiya sakamakon matsalar zafin rana mai tsananin gaske, inda ake sa ran adadin zai karu nan gaba.

https://p.dw.com/p/1FWBS
Hitzewelle in Indien
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Adhikary

Wani zafin rana mai tananin gaske ya hallaka mutane fiye da 430 a wasu jihohi biyu da ke kudancin kasar Indiya inda zafin ya kai wajejen maki 50 a ma'aunin selsuss abun da ya sanya motocin haya na Calcutta suka takaita ziraga-zirga a cewar hukumomin yankin a wannan Litinin. Sun ce adadin da aka bayar na iya karuwa nan gaba, ganin cewa har kawo yanzu ba'a samu sakamakon wasu yankunan ba, sannan kuma zafin baya nuna alamun ragewa.

Tun dai yau da 'yan kwanaki ne ake fuskantar zafi mai tsananin gaske a sassa daban daban a Indiya har ma a New Dehi babban birnin kasar inda zafin ya kai maki 45 a ma'aunin Selsuss, abun da ke haddasa katsewar wutar lantarki mai yawan gaske, ko ma da yake lamarin yafi kamari a jihohin Telangana da ke Kudancin kasar da Andhra Pradesh inda nan ne aka fi sahan wahalhalu sakamakon zafin, ind hukumomi ke ta yin kira ga al'umma da subar ayyuka cikin rana, bayan da aka samu rasuwar mutane 246 a wannan jiha.