1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Liberia

November 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvM2

A yau alúmar kasar Liberia ke kada kuriá a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Yan takara biyu dake neman kujerar shugabancin kasar George Wear shahararren dan wasan kwallon kafa da kuma tsohuwar ministan kudi ta Liberian Ellen Johnson kowanne na fafutukar samun rinjaye. Mutane fiye da miliyan daya da dubu dari uku wadanda suka yi rajistar sunayen su zasu kada kuriár a mazabu 3, 070 da aka tanadar a fadin kasar. Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya bukaci alúmar kasar su kada kuriár lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba. Ana fatan samun cikakken sakamakon zaben cikin makwanni biyu. A zaben farko da aka gudanar na ranar 11 ga watan Oktoba babu wanda ya sami adadin kuriun da ake bukata ta samun rinjaye.