1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dar-dar a Sudan ta Kudu

December 17, 2013

Harbe harben bindiga a Sudan ta Kudu sun janyo mutuwar akalla mutane 12, yayin da wasu da dama kuma suka sami rauni.

https://p.dw.com/p/1Aay9
Hoto: Reuters

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta bayyana sake barkewar harbe harbe cikin dare a babban birnin kasar na Juba, a dai dai lokacin da rundunar sojin kasar ke kokarin kawar da burbushin bangaren sojojin da hukumomi suka zarga da yunkurin juyin mulki a karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ministan harkokin wajen Sudan Ta Kudu Barnaba Marial Benjamin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewar, sojojin kasar sun yi nasarar cafke shugabanin siyasa biyar bisa zarginsu da alaka da yunkurin juyin mulki, amma kuma har yanzu hukumomin na farautar karin wasu. Ya kuma kara da cewar, tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar da ake zargi da jagorantar yunkurin, har yanzu yana cikin buya.

Südsudan Juba Ausschreitungen UN 16.12.2013
Shugaba Kiir ya ce zai ga bayan 'yan tawayeHoto: Reuters

Babakeren tsofoffin 'yan tawaye

Dama dai shugaba Salva Kiir, ya dora alhakin abin da ya kira da suna yunkurin juyin mulkin ne akan dakarun sojin da ke biyayya ga Riek Machar, da ya sallama a cikin watan Yuli, lamarin da kuma, Marc Lavergne, kwararre a fannin siyasa da ke cibiyar nazarin harkokin ci gaba da kuma na kimiyya ta kasar Faransa ya ce daidaton harkokin mulkin a Sudan ne Salva Kiir ya kawar:

Ya ce "Kamar karamin juyin juya hali ne ya afku a Sudan ta Kudu sakamakon sallamar mataimakin shugaban kasar. A da sun hada kai da juna ne domin yakar 'yan Sudan ta Arewa, wadanda a yanzu suka rikide ya zuwa abokan gaba. A shekara ta 1991 'yan kabilar Nuer ta tsohon mataimakin shugaba Riek Machar ta cimma daidaito da kabilar Dimka ta shugaba Salva Kiir, bayan rashin jituwar da ta rutsa da mutane fiye da dubu 100. Saboda haka, baya ga hamayyar siyasar da ke tsakaninsu, akwai kuma ta kabilanci, kasancewar su ne kabilu biyu mafi rinjayen da ke tafiyar da harkokin Sudan Ta Kudu."

Südsudan Juba Ausschreitungen UN 16.12.2013
An tsaurara matakan tsaro a birnin JubaHoto: Reuters

Harin baya bayannan dai sun afku ne a hedikwatar tsaron kasar da ke tsakiyar birnin Juba, , inda a yanzunnan da ake magana, babu wani abin da jama'a ke gani akan titunan birnin illa manyan motocin sojoji, yayin da fiye da fararen hula dubu 10 kuma suka sami mafaka a sansanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake kasar. A cewar Martin Alia Lomuro, ministan kula da harkokin majalisar zartarwa a Sudan ta Kudu, akalla mutane 12 suka mutu tun bayan fadan da ya faro a cikin daren Lahadi galibinsu kuma sojoji ne, yayin da wata tashar rediyon kasar kuma ta ruwaito cewar, akalla mutane 130 da suka samu rauni sakamakon fadan, ke samun kulawa a asibiti.

Makomar demokaradiya a Sudan ta Kudu

+b+Dama tun a wannan Litinin ce, shugaba Salva Kiir, wanda ya bayyana a gaban manema labarai sanye da kakin soji, sabanin tufafinsa na al'ada dake zama bakar kwat da hular malafa, ya yi alkawarin gano wadanda ke da alhakin kai harin, wanda kuma ya sa manazarta irinsu Annette Weber, shugabar sashen Afirka da yankin Gabas Ta Tsakiya a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa da kuma sha'anin tsaro ta Jamus bayyana cewar takaddamar ka iya taimakawa bullar jam'iyyun siyasa da dama, wadanda kuma ka iya inganta tsarin Dimokradiyya a kasar:

Ta ce "A tsakanin tsarin gwamnatin ne kowane bangare ke son ballewa, bayan sun kasance abokan kawance a yaki, a yanzu sun rikida zuwa abokan gabar siyasa. Sun dade suna gwabza yaki, saboda haka ba su kware a fagen siyasa ba, abin da yasa a yanzu suka gaza fahimtar juna."

Kwararriyar ta ce sabon yanayin zai kalubalanci kane kanen da jam'iyyar SPLM ta yi akan mulki, kasancewar lamarin ya zo ne jim kadan bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana kudirin yin takarar shugabancin kasa a shekara ta 2015.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani