1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman sulhu kan rikicin gabashin Ukraine

Ahmed SalisuDecember 24, 2014

Nan gaba a yau ne Rasha da Ukraine da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha gami da jami'an kungiyar tsaro da hadin kan Turai ta OSCE za su yi wani zama na sulhu.

https://p.dw.com/p/1E9Ys
Terffen zwischen Poroschenko und Lukaschenko in Kiew
Hoto: Reuters/Ukrainian Presidential Press Service/Lazarenko

Tattaunawa tsakanin bangarorin dai a 'yan makonnin da suka gabata ta sha fama da cikas, to sai dai a wannan karon masu shiga tsakani a tattaunawar wadda za ta wakana a birnin Minsk na kasar Belarus na son ganin an samu cigaba mai ma'ana.

Zaman na yau dai na zuwa ne bayan da Rasha ke cigaba da yin jan ido dangane da aniyar da Kiev ta dauka na shiga kungiyar tsaro ta NATO, shirin da shugaban Ukraine din ya ce ba gudu ba ja da baya.