1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Isra'ila ta neman zaman lafiya

Abdourahamane HassaneMarch 4, 2015

Dubban jama'a Yahudawa da Larabawa sun gudanar da wani gangami a gaban majalisar dokokin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1El96
Israel Frauen demonstrieren für Frieden
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Sebastian Scheiner

Masu gangamin sun yi shi ne da nufin tilasta wa duk wata gwamnatin da za ta zo kan mulkin bayan zaɓuɓɓukan da za a yi a ranar 17 ga wannan wata na Maris, da ta ba da fifiko ga shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Masu aiko da rahotanni sun ce duk da ruwan sama da aka riƙa sheƙawa kamar da bakin ƙwarya, wakilai na ƙungiyoyin mata sun kafe a bakin majalisar suna sauraran jawaban da aka gabatar.