1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin 'yan siyasa a Ghana

Jamila Ibrahim Maizango/AHSeptember 16, 2015

Ƙungiyoyin farar hula da na 'yan siyasa da na adawa na yin matsin lamba ga gwamnatin domin yin sabuwar rejista gabannin zaɓen shekarun 2016.

https://p.dw.com/p/1GXVf
Wiederwahl John Mahama in Ghana
Hoto: Reuters

Duk dai yunƙurin da hukumar 'yan sanda ƙasar Ghana ta yi na dakatar da zanga-zangar,ɗarurruwan jama'a ne suka hallara a dandalin Obra Spot da ke Circle a nan birnin Accra. Inda ƙungiyoyin suka gudanar da gangami don yin kira ga gwamnatin da ta yi sabuwar rejistar kafin zaɓen baɗi.

An bankaɗo kura-kurai a cikin rejistar waɗanda suka wuce kima.

Hakan dai na zuwa ne biyo bayan ƙalubalantar ingancin rejistar da mataimakin mai jan ragamar babban jam'iyyar ƙasar ta NPP Dr Mahmudu Bawumia ya yi, na cewar an bankaɗo wasu bayanai da ke nuna sunayen al'umma da ke cikin rejistar ya wuci kima, ciki ma dai har da baƙi. Na hira da David Asante, shugaban haɗakar ƙungiyoyin baƙi, ga kuma bayanin da ya yi.'' Shakka babu, dimukraɗiyyar ƙasar Ghana na daga cikin ababan da nahiyar Afirka ke tinkaho da su, kuma matakin na yau na daga cikin yunƙurin tabbatar da ɗorewa da bunƙasa dimukraɗiyya, saboda mun ga yadda maguɗin zaɓe ya hargitsa wasu ƙasashen Afirka.''

Wiederwahl John Mahama in Ghana
Hoto: Reuters

' Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa a gangamin

Bayan fara zanga-zangar 'yan sanda suka fara harba bindiga na gargaɗi tare da watsa wa jama'a barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi har ma a cikin gidajen jama'a, sakamakon yunƙurin fidda shingayen da 'yan sanda suka yi a kan tituna. Lamarin da ya jikkata da dama, wasu kuma suka suma. A ɗayan hannu dai, ɓangaren adawar ƙasar NPP, ya ce, akwai buƙatar ƙarfafa wa matakin domin kuwa ɗorewar dimukraɗiyyar.Na kuma jiyo ta bakin Salihu Yahaya Bo ɗaya daga cikin 'Yan siyasar ga abin da yake cewa.''Hukumar zaɓen ƙasa, tun a farko bayan tattaunawa da ɓangarorin adawar biyu ta ba da wa'adin zuwa ranar 22 ga watar Satumban nan, da muke ciki wa jam'iyyun , da su gabatar da shawarwari da suka tsayar a game da batun rejistar, kana ta ɗau wani mataki.''

Wiederwahl John Mahama in Ghana
Hoto: Reuters