1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da Boko Haram a Nijar

February 17, 2015

Dubban mutane ne suka fita wani gangami ranar Talatannan dan nuna adawa da ayyukan masu tada kayar bayan Boko Haram a Nijar mai makwabtaka da Najeriya.

https://p.dw.com/p/1EdDU
Niger Proteste gegen Mohammed Karikaturen in Charlie Hebdo 16.1.2015
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Firaminista Birgi Rafini na kasar ya jagoranci wannan gangami da aka gudanar da shi karkashin sanya idanun jami'an ‘yan sanda, inda wasu gwanayen iya harbi daga nesa suka zauna cikin shiri a saman gidaje dan zama cikin shirin ko ta kwana.

Dubban mutane ne suka fita wannan gangami yau Talata dan nuna adawa da ayyukan masu tada kayar bayan Boko Haram a Nijar

Wannan gangami da mutane dubbai suka fita sun rika daga kwalaye masu dauke da rubutun nuna kyama ga ayyukan na Boko Haram wacce tuni Firaminista Rafini ya bayyana ayyukanta da cewa basu da alaka da addinin Islama.

Kungiyoyi na 'yan kasuwa da dalibai da ma masu zaman kansu sun fita dan nuna goyon bayansu da adawar da ake da kungiyar wacce ayyukanta tuni sun hallaka mutane sama da dubu goma sha uku a Najeriyar dama wuraren da take kai hari a makotan kasar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita. Umaru Aliyu