Zanga-zangar adawa da G5 Sahel a Bamako
May 23, 2019Bayan da suka gicce babbar hanyar da ke zuwa sabuwar hedikwatar rundunar ta G5 Sahel daga bisani masu zanga-zangar sun kuma kafa runfunan a gaban cibiyar inda suka shiga zaman dirshen wanda suka ce za su kwashe kwanaki biyu suna yi.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito Mariam Keita wakiliyar kungiyar matan sojojin Mali, daya daga cikin masu zaman dirshen din na cewa ba sa kaunar ganin sojojin rundunar ta G5 Sahel a birnin na Bamako, su tattara su koma a yankin arewacin kasar ta Mali da ke zama filin daga, idan dai har da gaske suke cewa suna yaki ne da ta'addanci.
An maido da hedikwatar rundunar ta G5 Sahel ne a birnin na Bamako ne bayan harin da 'yan ta'addan suka kai a cibiyarta ta farko da ke a birnin Sevare na tsakiyar kasar a ranar 29 ga watan Yunin bara.