1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da gwamnati a Guinea

Yusuf BalaApril 20, 2015

A cewar tsohon firaministan ƙasar Sidya Toure na jami'iyyar UFR an samu nasara a wannan fitowa da ta yi sanadin tsaida komai a birnin Conakry.

https://p.dw.com/p/1FBMa
Proteste in Conakry, Guinea
Hoto: AFP/Getty Images/C. Binani

A ranar Litinin ɗin nan jami'an tsaro da dama sun bazu a titinan babban birnin ƙasar Guinea a dai dai lokacin da gungun masu fafutuka da ke adawa da gwamnati suka sake fita zanga-zanga bayan wata taho mu gama da jami'an tsaro da ta yi sanadin rasa rai a makon da ya gabata.

Bayan kira da a yi fatali da tsarin shirin zaɓen ƙasar mai cike da cece ku ce ɗaruruwan masu zanga-zanga sun riƙa kona tayoyi da shingaye da aka kafa a titunan birnin Conakry.

'Yan sanda dai sun mai da martani ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye abin da ya jawo wata taƙaitacciyar taho mu gama da masu zanga-zanga. A cewar wata majiyar gwamnatin ƙasar wani ɗan sanda da ke samun horo ya sami mummunan rauni bayan harbi da ya sha a lokacin kafsawar da masu fafutukar, an kuma kama wasu masu zanga-zangar guda biyu.