1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar goyon bayan gwamnatin Tunisiya

February 16, 2013

Dubbanin magoyan bayan jam'iyar Ennahda mai mulki a ƙasar Tunisiya, sun shirya tafiyar jerin gwano a birnin Tunis, domin nuna goyan baya ga gwamnati.

https://p.dw.com/p/17fZC
Hoto: Reuters

Tun ranar shida ga watan Fabarairu da mu ke ciki gwamnatin Ennaha ta sami kanta cikin wani mummuman rikici, bayan kisan gillar da wasu 'yan bindiga su ka yi wa madugun 'yan adawa Chokri Belaid. Masu zanga-zangar sun yi ta rera kalamomi masu zargin kafofin sadarwa da kasar Faransa da rura wutar rikicin ƙasar Tunisiya. Wannan tafiyar jerin gwano ta wakana ne  a yayin da Firaminista Hamadi Jebali, ke ƙoƙarin girka sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Tun bayan kifar da mulkin tsofan shugaban ƙasar Tunisiya Zin el-Abedin Ben Ali, wannan shine rikicin siyasa mafi muni da ƙasar ta fuskanta.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas