1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kungiyoyi a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH
August 7, 2017

Gamaiyyar kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zanga da ma zaman dirshin a Abuja akan bukatar lallai a bayyana musu zahirin halin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke ciki.

https://p.dw.com/p/2hp8T
Protest  Nigeria  (DW/U.A.Idris)
Hoto: DW/U.A. Idris

Duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka ta yi a birnin na Abuja, matasan sun gudanar da zanga-zangar suna cewar shiru game da halin da shugaba Buhari ke ciki ya isa haka. Ko da yake masu zanga-zangar na nanata batun yawan kwanakin da shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya kwashe yana a birnin London inda yake jinya, amma masana harkokin shari'a na bayyana cewar babu laifi tun da ya mika ragamar gudanar da mulki ga mataimakinsa, ko me za su ce a kan wannan. Charles Oputa ya ce akwai sake a lamarin.

Protest Nigeria Präsident Buhari
Hoto: DW/U.A. Idris

Abu ne da aka saba a ce shugaban kasa ya kwashe watanni uku baya cikin Najeriya amma ba wanda ke cewa komai, ba wanda ya san komai ba wanda ya san matsalar da ake ciki, bayan kuwa abubuwa sun tsaya, ga talauci a kasa, sannan mu ci gaba mu ce komai na tafiya dai-dai.

Har zuwa lokacin da suka kammala zanga-zangar tare da komawa dandalin ‘yanci inda suka sha alwashin ci gaba da zaman dirshin na sai baba ta gani babu wani jami'in gwamnati da ya fito ya karbesu a kan bukatar. Mukadashin shugaban Najeriya dai ya kafa kwamiti don bincikar lamarin, Sai dai masu fafutukar sun ce dole ne a bayyana musu gaskiyar abin da ke faruwa.