1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar salon yaki da cin hanci a Najeriya

Abdul-raheem Hassan | Uwais Abubakar Idris
October 17, 2017

Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Abuja, sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ke kauda ido na hukunta wasu jami'anta da ake zargi da cin hanci lamari da ke haddasa kokonto kan yaki da cin hanci da ake yi a kasar.

https://p.dw.com/p/2m26n
Nigeria Proteste gegen Muhammadu Buhari in Lagos
Hoto: DW/S. Olukoya

Kungiyoyin kare hakin jama’ar sun gudanar da zanga-zanga da zaman dirshin na wasu sao’i a Abuja, bisa abin da suka bayyana damuwarsu kan rashin daukan matakin da shugaban kasar ke yi a kan batutuwa na cin hanci da rashawa da suke ganin lamarin na wuce gona da iri. Kungiyoyin sun zargi gwamnatin Najeriyar da rashin daukar matakan ba sani ba sabo kan wasu laifukan cin hanci da rashawa da ake tuhumar wasu manyan jami'anta da yin babakere da dukiyar kasa.

Women's March in Nairobi Kenia
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Gamayyar kungiyoyin da yawanci magoya bayan shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne kafin ya ci zabe, su ne a yanzu ke nuna halin kai makura da ya kai su ga gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rashin tsawatarwa, musamman rashin zartas da hukunci kan tsohon Sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar bisa zargin cin hanci da kuma wasu jerin cuwa-cuwa na ba da ayyukan kwangila ba bisa ka'ida ba a ma'aikatar man fetur na kasar, wanda ya haddasa cece ku ce da tsamin dangantaka tsakanin karamin ministan albarkatun mai da shugaban hukumar NNPC a baya-bayannan. 

Wahl in Nigeria
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Tafiyar hawainiya da batun yaki da cin hanci da rashawa ke yi ba kawai ga binciken da aka gudanar bisa zargi ba, har ma ya zuwa kotu, na ci gaba da zama babbar matsala da ma kalubalen da ke fuskantar yakar cin hanci a kasar. Masu zanga-zangar dai sun yi alkawarin ci gaba da zaman dirshin har sai baba ta gani a kowa ce rana a dandanlin ‘yanci da ke birnin Abuja. 

Abin jira a gani dai shi ne ko zanga-zanga da zaman dirshin irin wannan, zai yi tasiri daga gwamnatin musamman na fitar da sakamakon rahotannin bincike a kan zargin cin hanci da rashawa da ya zamewa Najeriyar daya daga cikin babbar matsalar da ke kawo cikas ga ci gaban kasar.