1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-Zangar 'yan fararen hula a Nijar

Salissou BoukariJune 6, 2015

Dubban mutane ne suka fito kan tituna a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar domin amsa kirar kungiyoyi 38 na fararen hulla na nuna adawa da wasu manufofin gwamnati .

https://p.dw.com/p/1Fcl3
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne sun yi jerin gwano daga dandalin "Toumo" zuwa harabar majalisar dokoki da ke tsakiyar birnin Yamai dauke da kwalaye masu rubutu da ke sukar gwamnatin kasar. Wasu kuma masu zanga-zangar ta Nijar sun daura jan kyalle a wuyansu suna furta kalaman nuna adawa da matakan gwamnatin ta Nijar na yawan kame 'yan farar hula.

Tun dai 'yan makwannin da suka gabata ne kungiyoyin 'yan kasuwa suka soma sa kafar wando guda da gwamnatin, tare da neman soke wata yarjejeniya da gwamnatin ta Nijar ta yi da wani kanfanin kasar Faransa na Bolore da ke kawo cikas a harkokinsu na kasuwanci. Sannan kuma masu zanga-zangar na zargin gwamnati ta Nijar da lalata dukiyar kasa, da kuma amincewa da girka rundunonin sojoji na kasashen Faransa da na Amirka a cikin kasar.

Hakan dai na faruwa ne kasa da shekara guda da gudanar da zaben shugaban kasar ta Nijar da kuma na 'yan majalisar dokoki.