1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin hadin bakin sojoji a rikicin Boko Haram

Usman ShehuJune 4, 2014

Sojojin Najeriya na tsaka mai yuwa a rikicin da ke faruwa a kasar, inda ake tuhumar wasunsu da taimakawa ayyukan tarzuma, wanda ya addabi arewacin kasar

https://p.dw.com/p/1CCMu
Mali ECOWAS Truppen aus Nigeria in Bamako Archiv 19.01.2013
Hoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

Wasu rahotannin da kafafen yada labaran Najeriyan suka fitar sun bayyana cewa, a halin da ake ciki rundunar sojan kasar na yi wa wasu manyan hafsoshin soja shari'a a kotunan soja, bisa zargin da ake yi musu na hada baki da kungiyar Boko Haram, sai dai rundunar sojan Najeriya da ma gwamnatin kasar tuni suka karyata labarin.

A cewar jaridar Leadership, daya daga cikin manyan jaridu da suka fi suna a Najeriya, wanda kuma take daya daga cikin wadanda suka wallafa labarin. Jaridar ta ce a yanzu kimanin manyan sojoji masu mukamin janar su goma ake yi wa shari'a a kotunan sojojin Najeriya. To amma jaridar ba ta fadi sunaye sojojin, ko kuma wuraren da ake yi wa wadannan manyan hafsoshin sojojin shari'a. Don haka a hirar da muka yi da shi Kanal Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya, ya ce yana da shakku a ce akwai hannun sojan Najeriya bisa danyen aiki da kungiyar Boko Haram ke aiktawa.

To amma ko dai babu hannun sojan Najeriya da suke agazawa kungiyar Boko Haram, amma akwai rashin gudanar da nauyin da ya rataya a kansu ko kuma gwamnatin Tarayyar, da ke da alhakin magance wannan matsala ta Boko Haram. Domin kuwa duk da batun agazawa Najeriya da aka ce wasu kasashe kamar Amirka na yi, amma a hirarsa da tashar DW, Kanal Frederick Peterson III. mai ritaya, wanda mai baiwa gwamnatin Amirka shawara ne kan al'amuran yan ta'adda, kana mai sharhi kan alamuran tsaro, ya ce babbar matsalar a Najeriya ita ce rashin fada da cikawa.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau 12. Mai
Hoto: picture alliance/AP Photo

"A daya hannun mun nuna anniyarmu ta yin aiki da halatacciyar gwamnatin kasar wajen kwato 'yan matan Chibok, a daya gefen kuma mun samu tabbaci daga gwamnati cewa, ana hada hannun da gwamnatin Najeriya don kwato 'yan matan, amma abin da muka gani a kasa ba mai yawa ba ne, wajen gano da kuma kubutar da 'yan matan."

Babban abin da mutane irinsu Kanal Dangiwa Umar suke ganin yakamata a yi dai shi ne, gwamnatin Najeriya ta bar shure-shure ta samarwa sojojinta kayan aiki kawai, domin kuwa duk jarumtakar soja sai yana da makami. Abin da kuma kawo yanzu ba a kai ga ganin shirin da gwamnati Najeriya ta yi ba, duk da makudan kudaden da aka batar kan harkar tsaro.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal