1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin kitsa juyin mulki ya sa Turkiya a rudu

Suleiman Babayo/YBJuly 18, 2016

Dubban ma'aikata a kasar ta Turkiya dai sun rasa ayyukansu ban da wadanda aka kama biyo bayan wannan yunkuri na juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1JQwo
Bildkombo Fethullah Gülen / Tayyip Erdogan
Fethullah Gülen da Shugaba Tayyip Erdogan tsaffin abokai manyan abokan gaba a yanzuHoto: picture-alliance/Zaman/Reuters/M. Sezer

Babban abin da ya fito fili bayan yunkurin juyin mulkin na kasar Turkiya shi ne farin jinin Shugaba Racep Tayyip Erdogan ya karu, musamman saboda zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin kasar, amma abin tambaya shi ne akwai wasu muryoyin. Kristian Brakel masanin harkokin addinin Islama na cibiyar Heinrich-Böll ta Jamus da ke birnin Santanbul na Turkiya ga abin da yake gani:

"Akwai wasu muryoyi masu sukar gwamnati, amma ba kasafai ake gani a kan tituna ba, sai dai a kafofin sada zumunta na zamani. Akwai rarrabuwar kai sosai a cikin kasar. Wannan ya fito fili a dandalin sada zumunta na Twitter da aka bude guda biyu. Daya an nemi hukuncin kisa ga wadanda suka yi yunkurin kifar da gwamnati daga galibi masu kishin kasa. A daya hannun kuma ana cewa babu wani neman juyin mulki wasan kwaikwayo ne kawai, inda aka zargi gwamnati da kitsa abin da ya faru da kanta. Haka na nuna hadin kai da aka samu na kankanin lokaci ya wuce sakamakaon maganar juyin mulkin."

Brakel ya kara da cewa akwai jita-jita a Turkiya na hadin baki, wanda abu da aka saba fada kan komai. sai dai a wannan karo wani abu da ya fito fili shi ne goyon baya da gwamnati ta samu daga wadanda ba sa cikin jam'iyyar AKP mai mulki.

Türkei Unterstützer der Bewegung von Fethullah Gülen
Kokari na hana tofa albarkacin baki babban batu a TurkiyaHoto: picture-alliance/dpa/S. Suna

A nasa bangaren Michael Lüders mai sharhi kan harkokin yau da kullum kana masanin harkokin addinin Islama ya ce sojojin sun hango rashin nasara:

"Tun farko ya fito fili yunkurin kifar da gwamnatin ba zai samu nasara ba. Sojojin masu goyon bayan gwamnati suna cikin da wajen sojojin kasar wadanda suka samu nasarar mayar da zaman lafiyai."

Sai dai wani abin da masana suka amince zai yi wuya Fethullah Gulen mai ra'ayin Islama na da hannu cikin yukunrin kifar da gwamnatin ta Turkiya, kamayar yadda Shugaba Tayyip Erdogan ke ikirari. Sai dai a ganin Kristian Brakel masanin harkokin addinin Islama na cibiyar Heinrich-Böll matakan sun taimaka ga irin wannan tunani.

Türkei Putschisten werden festgenommen
An yi ta barin wuta a birnin Ankara kafin lamura du daidaitaHoto: picture-alliance/AA/Stringer

Tun bayan wannan yunkurin juyin mulki gwamnatin Shugaba Erdogan ta Turkiya ta samu goyon baya daga Shugaba Barack Obama na Amirka, da Shugaba Angela Merkel ta gwamnatin Jamus wadanda suka yi tir da matakin sojojin. Irin wannan goyon baya daga kasashen duniya zai taimaka wajen karafafa gwamnatin Turkiyar.