1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Zargin sojoji da kashe mutane

February 3, 2023

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam a Burkina Faso ta zargi sojojin kasar da kashe mutane sama da 25, ciki har da mata da jarirai a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/4N4Ol
Burkina Faso | Armee Putschisten Traore
Hoto: Kilaye Bationo/AP/dpa/picture alliance

Kungiyar mai suna CISC ta fitar da wata sanarwa inda ta ce a ranar Laraba ne wasu daga cikin iyayen wadanda abin ya shafa suka sanar da ita da kashe-kashen da sojoji kasar suka yi a kauyuka uku da suka hada da Piega, Sakoani da kuma Kankangou dake kusa da Fada N'Gourma.

Kawo yanzu dai ba a sami wani martani daga bangaren sojojin ko daga gwamnatin mulkin sojan kasar kan wannan kisa ba. To sai dai kungiyar ta ce tana ci gaba da tattara bayanai kan wannan aika-aika wadanda za ta shigar nan gaba a gaban kotu.

Burkina Faso dai na fuskantar kalubalen tsaro a shekarun baya-bayanan, lamarin da ya haddasa juyin mulki sau biyu a shekarar da ta gabata.