1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan fafutika na son a hukunta Issoufou Mahamadou

Salissou Boukari AMA
November 26, 2021

A Jamhuriyar Nijar kungiyar Tournon la Page ta nemi da a gurfanar da tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou a gaban kuliya bisa zargin tafka ta'asa a karkashin mulkinsa.

https://p.dw.com/p/43XQA
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: Presidence RDC/G. Kusema

A cikin kakausar murya kungiyar Tournons la Page mai fafutikar yaki da rashin gudanar da kyaukyawan mulki a kasashe reshen Nijar ta yi wannan sanarwa inda ta soma da jero tarin matsalolin da kasar ke fuskanta a fannin Ilimi, tsaro da sauran fannonin na jin dadin rayuwar al'umma. Ismael Haldi mamba ne a cikin wannan kungiya ta Tournons la Page Nijar.

Babban tsokacin da wannan kungiya ta yi shine na matsalar cin hanci da rashawa wanda ya mayar da hannun agogo baya a Nijar, sakamakon handama da babakere da ake zargin wasu tsaffin mambobin gwamnati ko 'yan kasuwa da aiwatarwa, inda kungiyar ta Tournons la Page ta yi da a soma da bai wa gawa kashi dan mai rai ya ji tsoro ta hanyar gurfanar da tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou. 

 Karin Bayani : Nijar shirin yaki da cin-hanci da rashawa 

Bildkombo Mohamed Bazoum und Mahamadou Issoufou
Mohamed Bazoum da Mahamadou Issoufou

DW ta yi kokarin jin ta bakin bangaran gwamnatin Nijar dan ta mayar da martani kuma Abdoulkader Mai Dalili daya daga cikin jami'an fannin sadarwa na fadar shugaban kasar Nijarya ce hadin kan yan kasar Nijar ne ta hanyar zama tsintsiya madaurinki daya ya kamata maimakon wani cece-kuce da ba zai kai kasar ko'ina ba.

Da karshe wannan kungiya ta Tournon la Page ta yi kira ga 'yan kasar ta Nijar musamman ma al'ummar birnin Yamai da su fito a ranar Lahadi biyar ga watan Disamba mai kamawa domin nuna bakin cikinsu da yanayin da kasar ke ciki, wanda suke ganin hakan zai zaburar da magabatan na Nijar daga koli wajen samarwa kasar mafita.