1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zawarcin Turkiya a yaki da IS

Yusuf BalaOctober 9, 2014

Kasashe da ke taron dangi wajen kawo karshen ayyukan kungiyar IS na ci gaba da neman goyon bayan Turkiya, wacce ake wa kallon mai ba da damar fatattakar 'yan IS din.

https://p.dw.com/p/1DSbU
Hoto: Reuters/Stringer

Wannan dai na faruwa ne ksancewar Turikiya makwabciya ga baki dayan kasashen da 'yan IS din suka addaba. Ana dai samun karuwar fargaba a kan iyakokin kasar da wadannan tsakanin kasashen da Turkiyar tun bayan da mayakan na IS suka fadada ayyukansu a kasashen Iraki da Siriya. A na ci gaba da gwabza fada taki kadan da iyakar kasar ta Turkiya da Siriya tsakanin masu kaifin kishin addinin da ke kara tunkarar garin Kobane na Kurdawa da dakarun Kurdawan.

Erdogan Vereidigung 28.08.2014
Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip ErdoganHoto: Reuters

Gabatar da bukatar shiga yakin gaban majalisa

Bukatar a gaban majalisar ta neman shigar Turkiya cikin yakin na hadaka a kan mayakan IS na ci gaba da zama wacce ba'a fayyace ta ba a dangane da irin rawar da kasar ta Turkiya za ta taka. Kasancewar bangaren adawa na ci gaba na nuna tarjiyarsa na cewa bada bakindsuba. Sai dai a bangaren shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ya nunar da cewa a shirye gwamnatinsa take wajen tunkarar duk wani nau'i na ta'addanci.

Babban kalubalen da ake ganin wannan kasa ta Turkiya na iya fuskanta kamar sauran kasashe da ke makwabtaka da inda mayakan na IS ke da karfi, shi ne maida martani kan kasar ta Turkiya ganin cewa ba da dadewa ba ne mayakan na IS suka sako wa kasar wasu al'ummarta da kungiyar ta yi garkuwa da su, amma a cewar Jens Stoltenberg wanda ke zama sabon sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, alhaki ne da ya rataya a wuyansu su bawa kasar kariya kamar ko wacce kasa.

Kurden demonstrieren in NRW gegen Gewalt in Kobane
Al'ummar Kurdawa na gudanar da zanga-zangaHoto: picture-alliance/dpa/Axel Vogel

Son ganin sojan Turkiya a fafatawar

Duk da cewa an gabatar da wannan bukata ta ganin sojan Turkiya sun tunkari duk wata barazana daga mayakan na IS fargabar da ake da ita na zaman martani daga shugaban kasar Syria Bashar al-Assad wanda tuni shugaba Reccep Tayyep Erdogan ke son ganin an sauke shi daga kujerarsa, a kan haka ne ma shugaba Erdogan ke kokarin ganin an yi kwaskwarima a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Erdogan dai ya bayyana shakku game da amfani kawai da hare-hare ta sama a kan mayakan na IS, ya kuma bayyana cewa ba zai tallafawa shirin da ba zai kawo karshensu ba, abun da ke sanya shakku cikin zukatan masu neman tallafin kasar ta Turkiya.