1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zida na yunkurin bai wa fararen hula iko

Pinado Abdu WabaNovember 15, 2014

Wannan ne yunkurin farko da gwamnatin rikon kwaryar sojin Burkina Faso ke yi na ganin ta mayar da mukamin na riko hannun fararen hula kafin zabukan badi idan Allah ya kaimu.

https://p.dw.com/p/1Do9Q
Burkina Faso - Oberst Isaac Zida
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Shugaban sojin rikon kwaryar Burkina Faso, ya ce ya maido da kundin tsarin mulkin da aka dakatar bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore sakamakon zanga-zangar al'umma.

Leftanant Kanar Isaac Zida wanda ya aiyana kansa a matsayin shugaban kasar ranar daya ga watan Nuwamba, ya ce ya kuma bai wa jagororin siyasar kasar daga yau zuwa ranar Lahadi su fitar da sunayen wadanda za a iya zaba, su maye gurbin shugaban da zai jagoranci kasar kafin zabe.

Da ma dai Kungiyar Tarayyar Afirka ta bai wa Zida wa'adin makonni biyu ya mika mukamin rikon ga fararen hula ko kuma ta kakaba mi shi takunkumi.

A ranar Lahadi sojojin kasar, da jam'iyyun siyasa, da fararen hula da shuwagabannin addini za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta bayar da suffar yadda gwamnatin rikon za ta kasance. Bisa tanadin wannan yarjejeniya, kwamitin da zai zabi shugaban kasa ya hada da sojoji biyar, 'yan adawa biyar, na hannun daman tsohon shugaban kasa biyar da kuma fararen hula da wakilan addinan kasar su takwas. Bayan an zabi wannan shugaban, ba zai iya tsayawa takara a zabuka masu zuwa ba, sai dai yana da izinin zaban sabon Firaminista, wanda shi kuma zai zabi majalisar ministocin da ya kunshi mambobi 25.