1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya fara ziyararsa a Kamaru

Yusuf BalaJuly 29, 2015

Sama da mutane dari shida ne suka halaka a Najeriya tun bayan da Buhari ya kama mulki a kasar yayin da Boko Haram a Kamaru kuma ta zafafa hare-harenta kan fararaen hula.

https://p.dw.com/p/1G77O
Kamerun Präsidenten Paul Biya & Muhammadu Buhari Nigeria
Shugaba Paul Biya da Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Shugaba Muhammad Buhari ya fara ziyararsa ta kwanaki biyu a kasar Kamaru dan sake dinke barakar da ke tsakanain kasashen biyu da ke zama makota ta yadda zasu hada karfi da karfe wajen fatattakar mayakan Boko Haram.

Wannan ziyara dai ta shugaba Muhammad Buhari da ke zama karon farko a Kamaru tun bayan hawansa kan karagar mulkin Najeriya a watan Maris da ya gabata, na zuiwa ne adaidai lokacin da kungiyar ta Boko Haram da ke yin mubayi'a da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama a kasashen Larabawa take zafafa hare-harenta a kasashen na Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar.

Da saukarsa a birnin Yaounde na kasar ta Kamaru shugaba Buhari mai shekaru 82 a duniya ya samu tarbar shugaba Paul Biya da mukarrabansa. Dukkanin shugaba tun da fari an tsara su gabatar da jawabi a ranar Laraba kafin jawabin hadin gwiwa da zasu yi a ranar Alhamis .

Kasar dai ta Kamaru ana mata kallon cewa zata sauya yadda take tunkarar yakin da wadannan kasashe da ke makwabtaka da tafkin Chadi ke yi wajan tunkarar Boko Haram a yayin da kungiyar ta sake aza kaimi da zafafa hare-hare a wadannan kasashe. Hare-haren da wasu ke wa kallon shure-shure da baya hana mutuwa.