1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIyarar Bush a Asia

Zainab MohammedNovember 15, 2005

Shugaban Amurka, wato George W Bush ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki bakwai a yankin Asia, a inda a yau ya fara yada zango a Japan

https://p.dw.com/p/BvUR
Hoto: AP

A yau ne shugaba George W Bush na Amurka ya fara rangadin aiki na Mako guda a yankin Asia.

Shugaban Amurkan dai ya fara da sa kafa ne a kasar Japan ,ziyarar da ake kyautata zaton zata inganta hullar Amurkan da kasashen Asia,musamman dangane da warware rikicin kera makaman nuclearn koriya ta Arewa da kuma tilastawa China aiwatar da sauye sauye cikin harkokin siyasa da tattali.

A gobe nedai ake saran Bush zai gana da premieyan japan Junichiro koizumi da sauran magabatan kasar kafin ya wuce kasar koriya ta kudu ,inda zai halarcui taron kungiyar kasashen yankin Asia da Pacifik,inda daga can zai zarce kasar Sin.

To sai dai saoi 24 kafin isan shugaban Amurka birnin Busan da ake gudanar da taron na kasashen yankin facifik da Asia,ayau jamian tsaro sunyi arangama da masu gangamin da suka hadar da manoma ,wadanda ke adawa da taron ,da ziyaran na Bush,wadanda ke kokarin wayar da kann mutane sama da dubu 100 domin yin zanga zangar adawa da taron na APEK.

A yanzu haka dai an dauki matakai tsaurara na tsaro a cibiyar gudanar da taron,inda aka watsa jamian yansanda dubu 46 a sassa daban daban na birnin ,domin samar da kariya wa shugabannin tattali na kasashen Asia da pacifik da zasu halarci wannan taro a koriya ta kudu.

An kuma dauki wasu matakai da suka hadar da haramtawa wasu yan kungiyoyi masu fafutukan neman yanci shiga cikin wannan kasa kiman in su 1,000,kana an sanya idanu wa wasu baki 400 idanu,domin kare kowane irin tashin hankali a yayin wannan taron.

Buigu da kari akwai rundunonin yansanda masu kwantar da tarzoma dake kewaye da harabar gudanar da taron,baya ga yandanda na kasa da kasa da tuni suka dauke da naurori na musamman dake ayyukan tsaro a sassa daban daban.

Tuni dai masu gangamin suka sanar da shirinsui na gudanar da wannan zanga zanga ,domin nuna adawa da bayyanar shugaba Bush na Amurkan,batu kuma da ake ganin zai iya juyawa mummunan arangama tsakanin yansanda da manoma da sauran alumma.

Wadanda suka ganewa idanunsu yamutsin na yau dai sun sanar dacewa ,manoman da sukayi gangamin na yau kimanin su dubu 12 sunyi ta jifan jamian yansanda,akan haryasu ta machi zuwa majalisar dokoki,domin bukatar soke dokar data bude kasuwan shinkafa.

Shugabannin kungiyoyin manoman dai sun sanar dacewa ,kimanin manoma dubu 50zasuyi jerin gwano zuwa Busan ranar jummaa,domin yin adawa da Bush da manufofinsa na yaki da ayyukan tarzoma musamman a Iraki,da kuma manufofin harkokin tattalin arziki a yankin Asia da facifik.