1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Najeriya zai ziyarci Nijar

Abdullaye Mammane AmadouJune 1, 2015

A wani matakin farko dai na ziyara izuwa kasashen waje shugaba Buhari ya zabi Jamhuriyar Nijer domin kai ziyararsa tare da tattaunawa da hukumomin kasar kan batutuwa da dama ciki harda batun tsaro.

https://p.dw.com/p/1FaCz
Mohammadu Buhari
Muhammad Buhari sabon shugaban NajeriyaHoto: Ekpei/AFP/Getty Images


A baya ga taya murna da farin cikin ganin an rantsar da Janar Muhamadu Buhari da wasu 'yan kasar ta Nijer ke yi, tare da kallonsa a matsayin gwarzon da shi kadai ke iya magance wasu matsalolin da ke shafuwar kai tsaye rayuwarsu ta yau da kullum bisa la'akari da matsayin da suke da shi na makwabtaka.

Ziyarar ta farko da Muhammad Buhari zai kai a Nijer kuma da zabar kasar Nijer a matsayin ta farko ya kara cusa farinjini da shaukin kaunarsa a wasu zukatan 'yan kasar ta jamhuriyar Nijer tare da kwana da sanin cewar har gobe kasashen na a matsayinsu na uwa daya uba daya ta fannin tattalin arziki da zamantakewar yau da kullum uwa uba batun yaki da mayakan Boko Haram da ya zamewa kasashen biyu munduwa a zukata, hasali ma masana na ganin wannan batun na yaki da Boko Haram da tshohon janar din sojan mai ritaya ya yi alwashin yakar sa da zuciya daya na daga cikin mahimman batutuwan da zasu tattauna akai da takwaransa mai masaukin baki Isufu Muhamadu.

Sake damara a yakar ta'addanci

Malam Yahuza Sadisu Madobi Ministan yada labarun Jamhuriyar Nijer ya ce wannan ziyara za ta tallafawa kasashen ta fiskoki da dama:

DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi
Yahouza Sadissou Mabobi ministan yada labarai a NijarHoto: DW/M. Kanta

"Nijer da Najeriya da sauran kasashen da ke kewaye da kogin Tchadi suna fuskantar matsalar mayakan Boko Haram, saboda hakan zasu tattauna game da yadda za'a kara zage damtse tsakanin kasashen nan gaba daya domin ganin yadda za'a fuskanci wannan matsalar sa'annan kuma a kwai batun tattalin arziki".


A nasu bangare dauko daga masana kimiyar siyasa har izuwa masu fashin baki ta fannin tsaro na ta sharhi kan irin yanda ziyarar ta shugaban kasa Buhari zata kasance a Nijer dama irin wata kila tallafin da zai nema daga mahukumtan kasar ta Nijer wajan cimma alwashinsa da yayi na yakar Boko Haram.

Boko Haram matsalar makotan kasashe
Dr Yusuf Yahaya malami ne a jami'ar Yamai kuma mai sharhi ne a fannin tsaro na mai ganin cewar ziyarar ta Buhari na Kunshe ne da godiya ga kasashen da suka kamawa kasar yaki da 'yan kungiyar:

Nigeria Soldaten in Diffa
Sojoji a yankin DiffaHoto: Reuters/J. Penney


"Bayan godiya da irin rawar da suka taka kuma zai dauki sandar soji ya yaki Boko Haram, kuma idan har ya yake su daga cikin wadannan kasashen guda hudu, biyu din nan su ne basu da karfi da Nijer da Kamaru idan 'yan Boko Haram sun matsu ta nan ne suke fita".


Tuni dai wasu manya manyan yan siyasar kasar suka fara nuna ganin lokaci yayi da takamata a ce daukacin kasashen da suke yaki da mayakan na kungiyar Boko Haram sun sauya salon tafiya ta kowane fanni idan har ana son a ciyo kan matsalar tsaron da ya zamewa kasashen alakakai, kamar yadda mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijer Ben Omar Mohamad ya bayyana.