1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban Jamus a Gabas ta Tsakiya

November 30, 2010

Isra'ila ta nemi Jamus ta shiga tsakani domin a samu zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/QLWL
Christian Wulff da Shimon PeresHoto: picture-alliance/dpa

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Jamus na da rawar da za ta iya takawa wajen warware rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin Gabas ta Tsakiya. A lokacin da ya gana da shugaban Tarayyar Jamus Christan Wulff a birnin ƙudus, Netanyahu ya ce Tarayyar Jamus za ta iya taimakawa a samu fahimta tsakanin Isra'ila da sauran ƙasashen yankin da suke taƙaddama da ita. 

Sai dai shugaba Wulff ya jaddada matsayin ƙasarsa a inda yayi kira ga ɓangarorin da ke gaba da juna da kai hankali nesa, tare da neman Isra'ila ta dakatar da gine-ginen wuraren share wuri zauna a zirin Gaza, da sune ummal'aba'isan cijewar tattaunawa. Firaminista Netanyahu na Isra'ila ya nunar da cewa a shirye ya ke ya koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da palesɗinawa.

A yau ne shugaba Wullf zai gana da shugaban Palesdinu wato Mahmoud Abbas a ci gaba da rangadin kwana huɗu da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou