1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zubewar kimar 'yan sandan Najeriya

August 15, 2013

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce wasu ma'aikatanta ne ke jawo zubewar kimarta ta yadda al'umma ba sa daukarta da mutunci a kasar.

https://p.dw.com/p/19QhU
Polizei in NigeriaHoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Mataimakin babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta shida Mr. Jonathan Johnson ne ya bayyana hakan a birnin Uyo na jahar Akwa Ibom yayin ganawa da rundunar 'yan sandan jahar, inda ya bayyana cewar da za a gudanar da cikakken bincike a tsakankanin 'yan sanda to kuwa za a fiddo da yan fashi da makami daga cikinsu a dalilin rashin godiyar Allah.

Mr. Jonathan ya ce za ka ga 'yan sanda kan tituna maimakon su yi aikin da ya kai su sai su bige da karbar kudade daga direbobi da kuma yin ababen da basu kamata ba, sannan a same suna hada baki da 'yan fashi da makami don ayi fashi da kuma sayarwa da muggan mutane makamai sannan ga halayyar cuku-cukun sauya bayanan masu kara a ofisoshins, baya ga baiwa muggan masu laifi bayanan da za su samu nasarar kashe 'yanuwansu 'yan sanda.

Polizeiposten in Nordnigeria
Shingen 'yan sanda na binciken ababan hawaHoto: Katrin Gänsler

DSP Ibrahim Tasiu, shi ne jami'in hulda da jama'a a ofishin mataimakin babban sipeton na 'yan sanda shiyya ta shidda din, kuma bayan tabbatar da jawaban mai taimakawa babban sifeton 'yan sandan na Najeriya na shiyyar ta su, ya yi karin haske kan jawabin mai gidana nasu ya gabatar a birnin na Uyo na jahar Akwa Ibom inda ya ce

''rundunar 'yan sandan Najeriya na da azamar duba kanta da kanta domin kaiwa ga yin waje da bata-gari daga cikinta. A matakin shiyya kuma muna da wani tsari na bin diddigin yadda 'yan sanda ke yin aikin kamar yadda ya kamata don kakkabe bata-garin da ka iya bata suna 'yan sanda ko zamewa al'umma hadari.''

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Sunturi na 'yan sandan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Baya ga matsalolin da mataimakin babban sifeto 'yan sanda na Najeriya ya nuna, a hannu guda ya koka kan yadda 'yan sanda ke shiga tawagar wasu masu hannu da shuni ko kuma kamfanoni a Najeriya da nufin yin aikin tsaro ba kuma tare da samun umarnin yin haka ba daga shugabanninsu.

Su ma dai al'ummar yankin na Uyo sun tofa albarkacin bakunansu dangane da hallayar ta 'yan sandan Najeriya da ma dai yadda su ke tafi da aiyyukansu wanda a cewar mutanen abu ne da za a yi Allah wadai da shi.

Kan dai wadannan dimbin matsaloli da ke tattare da wasu 'yan sandan na Najeriya da kuma ke zubda mutuncin aiki ne ya sanya Mr. Jonathan Johnson ya tabbatar cewar rundunonin 'yan sanda da ke shiyya ta shidda wadda ya ke jagoranta sun tashi haikan wajen yakarsu.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Ahmed Salisu