1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma ba zai jagoranci babban taron ANC ba

Abdul-raheem Hassan
July 11, 2017

Jam'iyar ra'aayin gurguzu wato SACP da ke kawance ga ANC mai mulki a Afiraka ta Kudu, ta sha alwashin takawa shugaba Jacob Zuma birki daga jagorantar babban taron jam'iyar na bana..

https://p.dw.com/p/2gLa5
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob ZumaHoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Jagororin jam'iyar kawancen sun bayyana matakin haramtawa shugaba Zuma gabatar da jawabin ne da nufin kaucewa tashin hankali da ka iya barkewa a yayin taron. Indai wannana yunkuri ya yi tasiri, to wannan shi ke zama karon farko da shugaba Zuma bai jagoranci babban taron jamiyar ba tun bayan darewar sa karagar mulki a shekara ta 2009.

A yanzu dai wasu kusohin jam'iyar shugaban wato ANC da sauran jam'iyun kawance, na zafafa kalaman bukatar sauke shugaban bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa, wannan ya sa shugabanni jam'iyar ke ganin dulmiyar da shugan ke ciki a yanzu, ya rage tasirin jam'iyar a tsakanin al'ummar Afirka ta Kudu.

Duk dai da cewa ana saura watanni 5 kacal shugaba Zuma zai kawo karshen wa'adin sa na shugabantar jam'iyar ANC da shugabancin Afirka ta Kudu, amma ana sa'ido wajen ganin tasirin kuri'ar yankan kauna da majalisar dokokin aksar za su kada kan shugaban a ran 8 ga watan Augustan da ke tafe.