1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma ya yi Allah wadai da hari kan baki

Pinado Abdu WabaApril 16, 2015

Mutane hudu ne suka hallaka tun da aka fara kai hari kan baki, makonni biyu da suka gabata a birnin Durban da ke Kwazulu-Natal.

https://p.dw.com/p/1F9iz
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: AFP/Getty Images/R. Bosch

Jami'an 'yan sandan Afirka ta Kudu sun yi ta harba harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna kyaman baki a birnin Johannesbourg, a daidai lokacin da shugaban kasar Jacob Zuma ya yi kira da a dakatar da irin hare-haren da ake kaiwa baki a kasar.

Kusan mutane 200 ne suka fito suna ihu suna wa baki gargadin cewa su koma kasashensu na asali ko kuma su gamu da gamonsu. Sun yi ta jefa duwatsu a kan motocin dake wucewa kan hanya da ma 'yan sanda a babban birnin cinikayyar kasar.

Shugaban kasa Jacob Zuma ya nuna matukar damuwarsa da wannan lamari ya mayar da martani ga rikicin a majalisar kasar yau da rana.

"Duk yawan takaici, ko fushin da al'umma ta yi, ba zai halatta irin hare-haren da aka kaiwa baki ba, da ma sata da kwasar ganimansu da aka yi. Mun yi Allah wadai da wannan lamari, domin hare-haren sun janyo zubewar martabar da aka san Afirka ta Kudu da shi".