1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zumuncin Musulmi 'yan Afirka a Jamus

Binta Aliyu Zurmi
January 2, 2018

A duk karshen shekara Musulmi 'yan asalin Afirka mazauna Jamus kan hadu don sada zumunci a tsakaninsu tare da gudanar da wa'azi da laccoci don fadakar da juna koyarwar addini tare da gudanar da liyafar cin abinci.

https://p.dw.com/p/2qDCt
Deutschland Oberhausen Moslem Gemeinde
A irin wannan taro na Musulman bana a Jamus a karshen shekara an yi wa'azi don tunatarwaHoto: DW/B. A. Zurmi

Da karatun na Al-qur'ani mai girma ne a ka bude taron na bana da ya gudana a garin Oberhausen na  jihar Nordrhein­ Westfalen wanda ya samu halartar Musulmai daga sassan kasar ta Jamus da ma wadanda suka halarci taron don sauraron wa'azi daga bakin malamai da suka gabatar da wa'azi da ya mayar da hankali wajan fadakar da al'ummar bukatar tashi tsaye wajen rike koyarwar addinin Islama bisa koyarwar Qur'ani da Hadisan ma'aiki (S.A.W).

Taron an shirya shi ne a karkashin inuwar kungiyar al'ummar Musulmi ta kasar Jamus, wacce aka fi sani da "Musulim Umma in Germany". Kungiya da ke aiki don hada kan al'ummar Musulmin 'yan asalin nahiyar Afirka mazauna Jamus.

Abdulmumin Yahaya Abbas wanda ke daya daga cikin malamai da suka gabatar da wa'azi a taron ya bayyana cewa duba da yadda Musulmai musamman 'yan asalin Afirka basu da rinjaye a kasar ta Jamus na daga cikin dalilai na shirya wa'azin a lokutan hutu don tunatar da mabiya koyarwar addinin.

Deutschland Oberhausen Moslem Gemeinde
Musulman da kan fito daga sassa na Jamus sun taru a bana a garin OberhausenHoto: DW/B. A. Zurmi

Shiekh Sulaiman shi ne babban limamim masalacin Masjudul Sunnah a birnin na Oberhausen, ya bayyana cewa baya ga wa'azin da kungiyar ta faro yau shekaru talatin, ana kokari na ci gaba da yada addinin a sauran sassa da ma gina wuraren ibadu.

Wasu daga cikin al'umma da suka halarci taron na wa'azin Tijjani Haruna Garba daga birni Dortmund da kuma malama Maryam da ke zama a garin na Oberhausen sun bayyana jin dadinsu da taron na bana da suka ce wata dama ce ta ganawa da 'yan uwa da abokan arziki.

Baya ga wa'azin da ake gudanarwa 'yan wannan kungiyar kan koyar wa yara addini a masallatai daban-daban kamar yadda wadansu yaran suka shaida. A karshen taron mahalartan sun gudanar da liyafar cin abinci irin na gargajiya wanda mahalartan suka ce ya tuna masu da rayuwar Afirka inda suka fito.