1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan gyaran tsarin shari'ar Poland

Mohammad Nasiru Awal AS
July 24, 2017

Shugaban Poland Andrzej Duda ya yi fatali da gyaran fuska da aka yi wa tsarin shari'ar kasar wanda ya janyo zanga-zanga a kasar sannan a bangare daya kungiyar tarayyar Turai ta yi barazanar sanya wa mata takunkumi.

https://p.dw.com/p/2h4R1
Andrzej Duda
Hoto: picture alliance/Pap/P.Supernak

Matakin hawa kujerar naki da Shugaba Andrzej Duda ya dauka ya zo da bazata, kasancewa shugaban na Poland babban mai dasawa ne da jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Law and Justice Party wato PiS mai jan ragamar mulkin kasar wadda ta jagorancin matakin yi wa tsarin shari'ar kwaskwarima.  Shugaba Duda ya ce ya dauki wannan mataki bayan tattaunawa mai tsawo da ya yi da masana harkokin shari'a a karshen mako, lokacin da dubun dubatan 'yan kasa suka bazama kan tituna a fadin kasar ta Poland suna kira ga shugaban da ya taka wa matakin biriki.

Polen Protest gegen Justizreform in Warschau
Dubban 'yan Poland sun yi zanga-zanga don nuna adawa da gyaran fuska da majalisar dokokin kasar ta yi wa fannin shari'aHoto: Reuters/Agencja Gazeta/K. Atys

A ranar Asabar da ta gabata majalisar dattawan Poland ta goyi bayan matakin yi wa tsarin shari'ar kwaskwarima amma dole ana bukatar rattaba hannun shugaban kasa. Yanzu dai za a sake komawa da batun gaban majalisar dokoki inda za a yi masa gyaran fuska sai dai za a bukaci rinjaye na kashi uku cikin biyar kafin daftarin ya zama doka amma jam'iyayar PiS ba ta da wannan rinjaye a majalisar dokokin.

Tuni wasu 'yan kasar suka nuna jin dadinsu ga matakin hawa kujerar nakin da shugaban ya dauka. Wannan dai shi ne karo na farko da Shugaba Duda ya saba wa Jaroslaw Kaczynski a fili. A shekarar 2015 Kaczynski ya nada Duda a matsayin dan takarar shugabancin jam'iyyar ya kuma rika yin biyayya ga tsauraran manufofinta. A halin da ake ciki tarayyar Jamus da kungiyar Tarayyar Turai suna bi-biyar abubuwan daka je su komo a kasar ta Poland za su kuma dauki matakin da ya dace da zarar lokacin yin haka ya yi.