1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Paparoma zai ziyarci Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya?

Theresa Krinninger/UANovember 3, 2015

Yakin basasan da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya raunana shirin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da ya gaza samun nasarar shawo kan al'amarin, balle ma a yi tunanin gudanar da zabe.

https://p.dw.com/p/1GytC
Catherine Samba-Panza
Shugaban rikon-kwarya Catherine Samba-PanzaHoto: Reuters

A yayin da shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Francis ya yi gargadi ga samun zaman lafiya da mutunta juna tattare da halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, gidaje suna ci gaba da konewa, mutane suna rasa rayukansu a birnin Bangui.

Wakilin DW da ke can, Jeff Murphy Bares, ya kidaya kimanin gidaje dari da aka kone da mutane uku da aka kashe, wasu 22 kuma suka samu rauni sakamakon tashin hankali a kwanakin nan, yayin da dubbai suke tserewa daga gidajensu. Dalilin wannan tashin hankali shi ne daukar fansa, a wannan karo daga Musulmai. Kafin haka Kiristoci sun kutsa wani yanki na Musulmai mai suna PK-5, inda suka kashe matasa biyu. Wasu mutane biyu da suka zo taimako, suma a nan suka rasa rayukansu. Wata da ke zaune a yankin, Melanie Andjokra ta rasa dalilin da ke sanya kashe mutane haka nan kawai.

Shugaban kasa ta rikon kwarya Catherine Samba-Panza ranar Litinin lokacin jawabi gaban manema labarai ta ce akwai alamu burin wannan tashin hankali da yaki ci, yaki cinyewa shi ne a raunana gwamnatin rikon kwarya, tare da manufar yi wa shirin Paparoma na kawo ziyara kasar kafar ungulu da kuma rushe shirin gudanar da zabe. A zahiri an fara tantama game da ko Paparoma Francis zai cika alkawarin kai ziyara Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a karshen watan Nuwamba. Kasar dai an shirya za ta kasance a jerin wadanda Paparoman zai yada zango lokacin tattakin kwanaki shida da zai yi a nahiyar Afirka. Lokacin jawabin da ya saba yi ranar Lahadi, Paparoman ya bayyana matukar damuwa da tashin hankali a kasar, inda ya nemi wadanda abin ya shafa su kawo karshen tashin hankalin.

Zentralafrikanische Republik Proteste und Gewalt in Bangui
Tashin hankali a Jamhuriyar Afirka Ta TsakiyaHoto: picture-alliance/AA/H.C. Serefio

Tashin hankalin baya-bayan nan ya zama ci gaba ne na rikicin da aka dade ana fama dashi a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Wata guda kafin hakan aka kashe mutane 42, lokacin harbe-harbe kan tituna a birnin Bangui, wasu daruruwa suka sami rauni, yayin da dubbai suka nemi mafaka a yankunan da Kiristoci suka fi yawa. Shugaban kasa ta wucin gadi, Catherine Samba-Panza, da ke jawabi ga manema labarai ta nuna takaicin kan abin da ke faruwa.

Bayan tashin hankalin na baya-bayan nan, mazauna Bangui sun hau kan tituna domin zanga-zangar neman shugabar wucin gadi Samba-Panza ta yi murabus, a kuma janye sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa. Wasu 'yan zanga-zangar sun so mamaye fadar shugaban kasa, abin da rundunar kiyaye zaman lafiya ta MINUSMA ta hana su yin haka. Daga baya Shugaba Samba-Panza ta ce hakan dai wani yunkuri ne na aiwatar da juyin mulki.

Räumung der Muslime in der Zentralafikanischer Republik
'Yan gudun hijira sakamakon yakin Jamhuriyar Afrika Ta TsakiyaHoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Yankin da ake kira PK-5 tun a karshen shekara ta 2013 zuwa farkon shekara ta 2014 ya zama dandalin kisan kare dangi tsakanin Kiristoci da Musulmai abin da ya zama tushen rikici gaba daya a kasar ta Afirka ta Tsakiya. Bayan juyin mulkin da kungiyar Seleka ta Musulmai ta yi wa gwamnatin Shugaba Francois Bozize a watan Maris na shekara ta 2013, Kiristoci suka kafa kungiyar mai suna Anti-Balaka. Daga nan aka shiga samun dauki ba dadi a duk fadin kasar tsakanin mayakan musulmai da Kirostoci.

A irin wannan hali na tsaka-mai-wuya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, maganar zabe ma ba ta taso ba. Tun da farko, zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki an shirya yi ranar 18 ga watan Oktoba, amma aka dage har zuwa watan Disamba. A bisa ta bakin Harve Ladsous, shugaban hukumar neman zaman lafiya ta Majalisar Dinkinj Duniya a kasar, tashin hankalin da ake ci gaba da samu da kuma lalata takardu da sauran kayayyakin zabe, ko kadan ba za su ba da damar gudanar da kada kuri'u a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba.