1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: 'Yan adawa sun yi watsi da jadawalin zabuka

Abdoulahi Maman Amadou/ GATAugust 1, 2015

'Yan adawar sun ce hukumar zaben kasar ba ta da hurumin tsaida jadawalin zabuka wanda yake a cewarsu aiki ne na hukumar sasanta rigingimun siyasa ta kasar wato CNDP.

https://p.dw.com/p/1G8AE
Aikin zabe a Nijar
Hoto: DW/M. Kanta

Jadawalin ya tanadi shirya zaben shugaban kasa a jimilce da na 'yan majalisar dokoki a ranar 21 ga watan Fabrairun shekara ta 2016. Zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a ranar 20 ga watan Maris 2016, kana zaben kananan hukumomi a ranar tara ga watan Mayu na shekarar ta 2016. Hukumar ta CENI ta gabatar wa gwamnati da jadawalin domin nazarinsa kafin tabbatar da shi a matsayin na dindindin.

Matsayin jam'iyyun adawa kan jadawalin

Sai dai kawancan jamiyyun adawar kasar na ARN ya nuna rashin gamsuwa da jadawalin da hukumar zaben kasar ta wallafa tare ma da zargin hukumar da yin shisshigi a cikin aikin da ba nata ba ne.

Honnorable Tijjani Abdulkadri shi ne shugaban rukunin 'yan majalisar dokokin kawancen adawa kuma sakataren jamiyyar MNSD Nasara mai adawa.

"Lalle lalle hukuma wannan ita ce ke aikin kamar na tsarin harhada kayan aiki da sauransu to amma tsaida ranakun zabe abu ne mai mahimmanci wanda taron hukumar sasanta rigingimun siyasa na CNDP shi ne yake bai wa gwamnati shawara a kai. Haka muka gada to amma sai muka ga ba a tsaida wannan ba kawai ta yi gaban kanta. Mu muna ganin karambani ne ta yi da shisshigi kawai da katsalandan, kuma babban izgili ne game tsarin tafiyar da zabe a kasar nan. Don haka wannan magana ba mu yarda da ita ba kuma hujjojin da suka bayar ba mu aminta da su ba"

Seini Oumarou madugun 'yan adawar Nijar
Hoto: AP

Matsayin bangaren masu mulki kan jadawalin

Sai dai a yayin da kawancen adawar ke fatali da jadawalin na zabe, shi kam kawancen jamiyyun da ke mulki murna ya yi da ganin irin wannan rana tare da nuna gamsuwarsa dari bisa dari ga sabon jadawalin zabe da hukumar ta wallafa.
Malam Tossa Yve Ali shi ne kakakin kawancen jamiyyun da ke mulki.

Niger Mahamadou Issoufou Präsidentschaftswahlen
Mahamadou Issoufou shugaban kasar NijarHoto: picture alliance/Photoshot

"To idan har 'yan siyasa ne kawai za su tsaida ranar zabe to don mi aka kafa hukumar ta CENI. Mine ne aikinta kenan, domin ita ce ke tsaida ranakun zabukan ta ce kuma ga abinda za a ba ta ta yi wannan aikin da aka sanya ta. Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa gwamnati ko awa guda ba za ta kara ba a kai.
Dan haka wannan jadawalin da hukumar ta fitar mu ya gamsar da mu
".


Yanzu haka dai hankalin 'yan kasar ta Nijar ya karkata a kan matsayi da matakin da gwamnati za ta dauka kan sabon jadawalin mai alamun sarkakiya da hukumar zaben ta wallafa. Tuni dai wasu masharhanta ke ganin hukumar ta shiga aikin da kafar hauni ganin irin yadda jamaa suka soma zargin wasu mambobinta da karbar na toshiyar baki daga wasu 'yan siyasa domin tsayar da jadawalin, zargin da hukumar ta karyata tare da cewar ta gudanar da bincike kuma ta gano wani ne dan siyasa ya zo don bai wa abukanin siyasarsa kudaden tallafi sai aka yi kuskure kudaden suka shiga hannun wani mai adawa da matakin. To amma hukumar ta ce ta sha alwashin kawar da duk wasu ababe masu nasaba da siyasa a ciki da wajenta.

Abdoulaye Mamane Amadou DW Hausa daga Niamey Niger