1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ya gana da Obama a fadar White House

Salissou Boukari
November 10, 2016

Sabon shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump, ya gana a wannan Alhamis din da shugaba mai barin gado Barack Obama a fadarsa ta White House domin tattauna batun shirye-shiryen mika mulki.

https://p.dw.com/p/2SVl9
USA Washington Treffen Obama und Amtsnachfolger Trump
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Duk da cewa a baya kadan mutanen biyu sun yi ta furta wa juna kalamai marassa dadi a lokcin yakin neman zabe, amma kuma ganin yadda 'yan kasar ta Amirka suka yanke hukuncin bai wa Donald Trump damar jan ragamar kasar ta Amirka, amma kuma a cewar Shugaba Obama babban burinsa shine na ganin sun tafiyar da dukannin tsare-tsaren mika mulki cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, kamar yadda hakan ta wakana da shi a baya lokacin da ya karbi mulki daga shugaba mai barin gado na wancan lokaci George Bush. A lokacin da yake taya Donald Trump murnar cin zabe, Shugaba Obama ya ce da farko dai su 'yan kasar Amirka ne kafin suke zama 'yan Democrate ko kuma 'yan Republicain, inda ya ce ya kyauttu su duka su tuna cewa dukanninsu gungun guda ne masu bukatar ganin ci-gaban kasar Amirka da al'ummarta baki daya.

Daga na ta bangare uwargidan shugaba Obama Michelle Obama, za ta gana da uwargidan Donald Trump Melania Trump da ke a matsayin uwargidan sabon shugaban kasar na Amirka yayin daga bisani mataimakin shugaban kasa mai barin gado Joe Biden shi kuma zai gana da sabon mataimakin shugaban kasar mai jiran gado Mike Pence. Donald Trump da tuni ya soma ayyukan kafa sabuwar gwamnatinsa, zai kuma gana da yammacin wannan rana ta Alhamis da shugaban majalisar wakillan kasar Paul Ryan wanda kuma ya ke dan jam'iyyarsa ta Republicain. Donald Trump dai na bukatar goyon bayan majalisun kasar biyu wajen tafiyar da mulkin na Amirka, inda ake ganin zai samu sauki sosai ganin cewa jam'iyyarsa ke da rinjaye a majalisun biyu.