1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Nijar na barazanar fadawa cikin rashin tabbas

Abdoulaye Mamane Amadou/MNAMarch 9, 2016

Bayan da kawancen 'yan adawa a Nijar ya dauki matakin janyewa daga zaben shugaban kasa zagaye na biyu, masharhanta sun ambato wani yanayi da kasar ke son fadawa ciki da ba a taba samun irinsa a tarihin kasar ba.

https://p.dw.com/p/1IA1m
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A dai lokacin da yake karanto sanarwar kawancen 'yan adawa na COPA 2016, Alhaji Seini Oumarou cewa ya yi sun yanke hukuncin kaurace wa duk wasu lamurra da suka shafi shirye-shiryen zabe kana sun kira wakilansu da su janye daga hukumar zabe da kira ga 'yan majalisun dokokin da su balle wa duk wani zaman aiki a majalisa.

Matakin dai da 'yan adawar kasar ta Nijar suka bullo da shi na a matsayin irinsa na farko a tarihin siyasar kasar da wani kawancen adawa ya fitar a yayin da ake dab da shiga zabe. Kana matakin da 'yan adawar suka bullo da shi ya zame wa wasu masu fashin bakin siyasa mataki irin na ba-zata bisa la'akari da shirye-shiryen zaben zagaye na biyu ya kankama.

Niger Präsidentschaftswahl Ergebnisse
Yanzu haka dai an bude yakin neman zabe na zagaye na biyuHoto: DW/K. Gänsler

To ko mi hakan ke nufi ke nan a dokance? Farfesa Djibril Abarchi malami a tsangayar shari'a ta jami'ar birnin Yamai ya yi karin haske.

"Wanda ya je zagaye na farin na zabe ya kawo koke-kokensa a gaban kotu kuma kotu ba ta lura da koke-kokensa ba, to ta ina kuma za ya je zagaye na biyu na zabe? To ko wane irin tasiri ne wannan matakin na janyewa da kawancen adawa ya yi zai yi? In Hama Amadou da zai je zagaye na biyu yayi wasiyar cewa ga shi ya janye kuma sauran a hukumance a rubuta takardar da ke nuna cewar eh lalle dan takarar ba ya da niyar zuwa. Sai a nemi na biyu da zai bi mishi, in baya zuwa a nemi wanda yake bi mishi, in shi ma ba ya zuwa, a ci gaba da nemo wanda yake bi mishi har a cimma wanda ya ce ya yarda a tafi takara."


Janyewar 'yan adawa ba zai hana gudanar da zabe ba

Sai dai su ma masu fashin bakin siyasa kamar su Farfesa Yusuf Yahaya malami a jami'ar birnin Yamai na mai ganin cewar matakin na 'yan adawa ba abin mamaki ba ne.


"Janyewar da 'yan adawa suka yi ba a taba yinsa ba ko lokacin da soja suke juyin mulki su ce a zo mu yi zabe. Kuma ina son a san da wani abu, janyewar 'yan adawa ba zai hana a yi zabe ba, domin akwai wadanda cin moriyarsu ne a yi zabe, ke nan ko ta halin kaka suna iya cewar a yi zabe don amfaninsu."

Niger Sitz der Fraktion der Oppositionspartei Moden Fa Lumana
Ofishin jam'iyyar Moden Lumana ta Hama AmadouHoto: DW/D. Köpp

Duk da yake ya zuwa yanzu matakin na COPA 2016 ya tsaya ne kawai ga sanarwa ba tare da aike da wata takarda daga dan takarar jam'iyyar ta Moden Lumana zuwa ga kotun tsarin mulki ba don bayyana matsayinsa na janyewa ga zaben na shugaban kasa ba a hukumance kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijar ya tanada. Wasu 'yan siyasar kasar na 'yan baruwanmu ire-iren su Sama'ila Amadou na jam'iyyar Awaywaya sun jinjina wa matakin da kawancen 'yan adawa ya dauka.


"Shi ne kawai mafitarsu, banda shi babu wata mafita fiye da hakan, ba wai maganar ba a son Issoufou ba ne, ko ba a son 'yan adawa. A'a maganar kasa ce da shi kanshi Issoufoun ya tsaya ya duba ya gani a duk lokacin da yake adawa wai an taba yin zabe irin wannan da yake mulki. To gaskiya shi ne da cewar wannan abun bai yiwa kasar nan kyau ba."


Wannan lamarin dai na a matsayin wani sabon babin da ya sake budewa a fagen siyasar ta Nijar mai kumshe da rikita-rikita kala-kala da kuma ake ganin kawowa karshensa zai dauki wani dogon lokaci.