1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙalubale ga Catherine Samba-Panza

October 15, 2014

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na nuni da cewar aƙalla mutane uku ne suka hallaka yayin da wasu ɗaruruwa suka ƙauracewa gidajensu.

https://p.dw.com/p/1DWC8
Hoto: Reuters

Ɗaruruwan mutane ne dai suka ƙauracewa gidajensu sakamakon wani sabon hari da tsagerun Ƙungiyar Anti-balaka suka kai a wani yanki da ke Bangui babban birnin ƙasar. Rikicin dai ya faro ne a kusa da gidan shugabar ƙasa Catherine Samba-Panza a yayin da 'yan Anti-balaka ɗauke da makamai suka farma gidajen mutane. Magajin garin gundumar Bangui din Joseph Tagbale ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar 'yan Ƙungiyar ta Anti-balaka sun kona gidaje 22 inda suka babbake wasu mutane biyu da ransu a cikin gidajensu. Babban Ƙalubalen da ke gaban Shugaba Samba Panza dai shi ne na tabbatar da daidaito da haƊin kan al'ummar Ƙasar da ke shirin darewa gida biyu sakamakon rikicin addini.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane