1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙalubalen da ke a gaban sabon firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

August 11, 2014

Mahamat Kamoun zai yi ƙoƙarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka cimma tsakanin Seleka da Anti-Balaka; tare da sake dawo da zaman lafiya a ƙasar.

https://p.dw.com/p/1CsZS
Zentralafrikanische Republik Interimspräsidentin Catherine Samba-Panza 23.01.2014
Shugaba Catherine Samba-PanzaHoto: Reuters

Shugabar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba Panza ta naɗa musulmi Mahamat Kamoun tsohon mai bai wa Michel Jotidiya shawara a matsayin sabon firaminista.

Mako ɗaya bayan murabus ɗin gwamnatin Andre Zapayeke da nufin kafa gwamanatin da za ta haɗa akasarin ƙabilun ƙasar kamar yadda yarjejeniyar birnin Brazaville ta tanada.

Taƙaitaccen tarihin Mahamat Kamoun sabon firaministan

Mahamat Kamoun mai shekaru 53 da haihuwa shi ne musulmi na farko da ya taɓa riƙe wannan muƙami na firaminista, tun samun yancin kan ƙasar. Mista Kamoun ƙwararre ne a ma'aitakar kuɗi, wanda ya taɓa riƙe muƙamin darakta kuɗi a lokacin Francois Bozize da aka kifar daga mulki a watan Maris na shekara ta 2013. Kana kuma ya yi zama daraktan fadar shugaban ƙasa a lokacin mulkin Michel Jotodiya tsohon jagoran Ƙungiyar Seleka daga shekarun 2013 zuwa 2014.

Brazzaville Versöhnungsforum 23.7.2014
Shugabar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tare da shugaban Kwango BrazzavilleHoto: Guy-Gervais Kitina/AFP/Getty Images

Ƙalubalen da ke a gaban Mahamat Kamoun ɗin na da yawan gaske

Mahamat Kamoun ya bayyana cewar Babban nauyi ne aka ɗora masa mai wahala idan aka yi la'akari da halin da ƙasar take ciki na taɓarɓarewar lamarin tsaro.

Zentralafrika Milizkämpfer Soldat 23.01.2014
Sojojin ƙasa da ƙasa na aikin kwantar da tarzomar jama'a a Jamhuriyar ta Afirka ta TsakiyaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

'' Sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbarta da doka na daga cikin abin da za mu fi maida hankali akai da farko. Abu na biyu shi ne taimaka wa 'yan gudun hijira na ciki da na wajen ƙasar su sake dawowa gida .''

Kafin zaɓen firaministan sai da shugaba Catherine Samba Panza ta nemi dukkan ƙabilun ƙasar su yi mahawara don zaɓar mutumin da ya dace.

Mawallafi : Salissou Issa
Edita : Abdourahamane Hassane