1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin haraji kan bankunan Jamus.

Halimatu AbbasMarch 22, 2010

Gwamnatin Jamus za ta ɓullo da sabon haraji akan bankuna

https://p.dw.com/p/MZXQ
Tsabar kuɗiHoto: DW

Gwamnatin  Jamus na shirin ɓullowa da ƙarin haraji akan bankuna a matsayin inshwara ga duk wata matsalar kuɗi da ka iya ɓullowa nan gaba. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta gana da jami'an ɗayan ɓangaren gwamnatinta ta gamin gambiza  game da wannan batu a jiya Lahadi. A wani zama da suka yi, jami'yyun da ke cikin gwamnatin gambizar su uku, wato Christian Democrat da Merkel ke wa jagora da Christian Social Union ta Hörst Seehofer da kuma Free democrats ta Guido westerwelle da dai sauransu sun daidaita kan ɗaukar sabon mataki game da dokokin da ke tafiyar da aikin bankuna da kuma ƙarin harajin da za a ɗora wa ma'aikatun kuɗi.  A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan telebijan, Volker Kauder, shugaban ɓangaren Merkel a majalisar dokoki ya ce gwamnatin ta amince da matakin daƙile biyan bashin bankunan da kuɗaɗen masu biyan haraji. Kauder bai dai yi ƙarin bayani game da yawan harajin da za a ɗora wa bankunan ba. Amma ya ce kuɗin zai yi biliyoyin euro.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala