1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaruwar ayyukan Alƙa'ida a Yamen

Usman ShehuAugust 6, 2013

An kakkaɓo wani jigin soji a yankin da ƙungiyar Alƙa'ida ke iko da shi a yammacin ƙasar Yamen

https://p.dw.com/p/19L7u
Yemeni soldiers stand guard outside the German embassy as Yemeni demonstrators protest against the kidnapping of nine foreigners and the killing of three in north-western Yemen, in the capital Sana?a, Yemen, 29 June 2009. Hundreds of Yemenis took to the street in Sana?a to denounce the kidnapping of a German family of five and British engineer who were taken at gunpoint along with two German theology students and a South Korean teacher while on a weekend excursion in the restive Yemeni province of Saada. The bodies of the two German female students and the South Korean teacher were found in Saada three days after the kidnapping. The fate of the German family and the British engineer is still unknown as army and security forces continue combing vast mountainous and desert areas in northern Yemen. EPA/YAHYA ARHAB +++(c) dpa - Report+++
Matakan tsaro da aka ɗauka a ƙasar YamenHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Yamen 'yan bindga sun kakkaɓo wani jirgin mai saukar ungulu wato na sojin, inda dukkan sojoji takwas da ke ciki suka mutu, ciki harda wani kwamandan sojojin. Rahotanni suka ce an kakkaɓo jirgin a yankin Wadi Ubida, inda ƙungiyar Alƙa'ida ta fi ƙarfi. Wannan harin ya zo ne a dai-dai lokacin da ƙasashen yamma ke nuna shakku a kan Yamen, tun bayan gargaɗin da Amirka ta yi na yiwuwar kai harin ta'addanci. Ƙasar Amirka dai ta fara ƙwace wasu daga ma'aikatanta daga birnin Sana'a babban birnin ƙasar ta Yamen. Rundunar mayaƙan saman Amirka ce ta fitar da ma'aikatan waɗanda ke aiki a ofishin jakadancin Amirka. Wannan kuwa shi ne matakin baya-bayan nan da ƙasar ta Amirka ta ɗauka, dangane da sanarwar da ta yi na rufe ofisoshin jakadancinta a wasu ƙasashen musulmi, a wani abin da ta ce wai ta samu bayyanai da ke nuna cewa ƙungiyar Alƙa'ida na shirin kai wa ƙasashen yamma harin ta'addanci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita. Abdourrahmane Hassane

AP