1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Philippines na fuskantar barazana

LateefaNovember 9, 2013

Mahaukaciyar guguwa da ta afkawa ƙasar na ƙara sanya fargaba ga al'ummar yankunan da abin ya shafa.

https://p.dw.com/p/1AEZB
Hoto: Reuters

A ƙalla mutane ɗari ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 100 suka jikkata a ƙasar ta Philippines, bayan da mahaukaciyar gugwuwa da ake yi wa laƙabi da "Haiyan" ta afkawa ƙasar.Sama da mutane dubu 750 ne dai suka ƙauracewa gidajensu, inda hukumomi da jami'an tsaro da na ba da agaji ke ƙoƙarin kwantar da hankula kan cewar za a ba su agajin gaggawa.

Wani Jami'i a hukumar kare afkuwar bala'oi ta Majalisar Ɗinkin Duniya Sebastian Rhodes Stampa, wanda a yanzu haka suka isa ƙasar domin ba da agajin gaggawa ga waɗanda bala'in guguwar ya shafa, ya ce mahaukaciyar guguwar ta ƙasar Philippines kusan iri ɗaya ce da annobar tsunami da yankin Asiya ya fuskanta a shekara ta 2004 inda kimanin mutane sama da dubu 20 suka hallaka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane