1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar EU ta ja kunnen Afganistan

Usman ShehuNovember 12, 2012

A wani matakin ƙosawa da cin hancin gwamnatin Afganistan, ƙungiyar Tarayyar Turai wato EU ta katse agajin Euro miliyan 20 da ta shirya baiwa ƙasar

https://p.dw.com/p/16hYN
Afghan President Hamid Karzai listens to U.S. Vice President Joe Biden, unseen, during a press conference in Kabul, Afghanistan on Tuesday, Jan. 11, 2011. (AP Photo/Musadeq Sadeq)
Hamid Karzai shugaban Ƙasar AfganistanHoto: AP

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta katse agajin da take baiwa ƙasar Afganistan na euro miliyan 20, inda ta yi gargaɗin cewa duk agajin tsabar kuɗi da za a baiwa ƙasar to dole sai an ga sauyi mai inganci. Jakadan EU a Afganistan yace tallafin Euro miliyan 20 da aka shirya baiwa ƙasar don inganta fannin shari'a, an dakatar da shine bisa rashin ganin hoɓɓasa daga mahukuntan Kabul. Jakadan yace EU na matuƙar bada mahimmaci wajen tallafawa ƙasar Afganistan, to amma nan gaba duk wani taimakon da za a baiwa ƙasar dole sai da sharruɗa. A watan Julin bana ne aka yi wani taron a birnin Tokyo na ƙasar Japan, inda ƙasashen duniya suka ɗauki alƙawarin tallafin sake gina Aghanistan nan da shekaru biyu masu zuwa. Jakadan EU yace babban dalilin daukar matakin shine, ɓangaren shari'an Afganistan ya gurɓace bisa cinhanci, abinda kuma ke shafar talakawan Afganistan da ma ƙasashe masu bada agaji don sake gina ƙasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Muhammed Nasir Awal