1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙurar rikici ta lafa a Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango, bayan an tabbatad da shugaba Kabila tamkar wanda ya lashe zaɓen ƙasar.

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubm

’Yan siyasa, daga duk ɓangarorin da ke hamayya da juna a Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango, sun yi kira ga kwanciyar hankali a ƙasar, bayan hukumar zaɓen ƙasar ta tabbatar da shugaba mai ci yanzu, Joseph Kabila, tamkar wanda ya lashe zaɓen.

Hukumar ta ce shugaba Kabila ya lashe zaɓen ne da samun kashi 58 da ɗigo 1 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da, yayin da abokin hamayyarsa a zaɓen na ran 29 ga watan Oktoba, Jean-Pierre Bemba, ya sami kashi 41 da digo 9.

A cikin jawabin da ya yi wa al’umman ƙasar a kan talabijin, jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen da Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta yi, shugaba Kabila ya yi kira ga duk ’yan ƙasar da su nuna haɗin kai da haƙuri da juna, a lokacin da ya biyo bayan zaɓen. Ya ƙara da cewa:-