1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙwarya-ƙwaryar tsagaita buɗe wuta a Gaza

November 20, 2012

Sojin Isra'ila guda ya mutu sanadiyyar makamin rokar da mayaƙan Hamas suka jefa, yayin da sassan biyu ke shirin fara aiki da yarjejeniyar sulhun da Masar ta jagoranta.

https://p.dw.com/p/16mxf
Mohammed Morsi, President of Egypt, addresses the 67th session of the United Nations General Assembly at U.N. headquarters, Wednesday, Sept. 26, 2012. (Foto:Jason DeCrow/AP/dapd)
Mohammed MorsiHoto: AP

A yayin da Isra'ila da Mayaƙan Falasɗinu ke ci gaba da musayar harbe harbe a yini na bakwai da fara rikici a zirin Gaza wanda ya haddasa mutuwar Falasɗinawa kimanin 130, kana da Yahudawa ukku, ƙasar Masar da ke shiga tsakani ta bayyana yiwuwar cimma yarjejniyar tsagaita buɗe wuta cikin sao'i ƙalilan masu zuwa, ko da shike kuma Isra'ila ba ta mayar da martani akan haka ba.

Shugaba Mohammed Morsi na ƙasar Masar, wanda ke shiga tsakani a rikicin Gaza na Falasɗinu ya faɗi bayan halartar jana'izar wata yar Uwarsa a lardin al-Sharqiyya da ke yankin arewacin Masar cewar ƙoƙarin shiga tsakani da nufin kawo ƙarshen rikicin zirin Gaza, na dab da cimma maslahar tsagaita buɗe wuta.

   Masu ruwa da tsakin da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu akan Gaza

Palestinian firefighters try to extinguish a blaze after an Israeli air strike on the Islamic National Bank building in Gaza City on November 20, 2012. Israeli leaders discussed an Egyptian plan for a truce with Gaza's ruling Hamas, reports said, before a mission by the UN chief to Jerusalem and as the toll from Israeli raids on Gaza rose over 100. AFP PHOTO/MAJDI FATHI (Photo credit should read MAJDI FATHI/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Sai dai kuma kakakin gwamnatin Isra'ila Mark Regev ya ce ba zai ce uffan ba game da wannan kalamin, yayin da wata tashar Rediyon Isra'ila kuwa ta ce wani jami'in gwamnatin Isra'ilar da tashar ba ta ambaci sunan sa ba ya shaida mata cewar akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a wannan Talatar, yayin da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta bi sahun sakatare janar na Majalisar Ɗinklin Duniya Ban Kin Moon daya ziyarci birnin Qudus. Tashar Rediyon ta ce tare da taimakon Jamus da Masar ne aka cimma yarjejeniyar, wadda kuma Isra'ila da Masar da kuma Amirka za su sanya ido akan yin aiki da ita, inda kuma ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi tsokaci akan yarjejeniyar.

Ya ce " Isra'ila na da 'yancin bada kariya ga al'ummar ta da kuma ƙasar ta. Babban abin farin ciki ne da a yanzu muka cimma matsayar neman hana yaɗuwar rikicin. Samar da zaman lafiya shi ne burin da muka sanya a gaba. "

Batun ƙoƙarin cimma yarjejeniyar dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta ta hanyar jiragen sama akan wasu yankunan zirin na Gaza, wanda ya sa adadin Falasɗinawan da suka mutu ya kai 14 a yinin. Hakanan sa'oi ƙalilan gabannin shugaba Morsi ya furta batun yiwuwar cimma matsayar tsagaita wutar, mayaƙan Hamas sun yi ta jefa makaman roka a birnin Qudus, da ke zama birnin na biyun da suke hari, birnin da kuma Isra'ila ta yi gaban kanta wajen ayyanawa a matsayin hedikwatarta.

     Rawar da Majalisar Ɗinkin Duniya wajen dakatar da rikicin Gaza

United Nations (U.N.) Secretary-General Ban Ki-moon (C) speaks during a news conference with Arab League Secretary-General Nabil Elaraby (R) after their meeting to discuss the situation in Gaza, in Cairo November 20, 2012. Ban on Tuesday called for an immediate ceasefire in the Gaza conflict, saying an Israeli ground operation in the Palestinian enclave would be a "dangerous escalation" that must be avoided. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS)
Ban Ki MoonHoto: Reuters

Tunda farko dai Ban Ki Moon ya miƙa buƙatar cimma maslahar ga sassan da lamarin ya shafa :

Ya ce "saƙo na a fili yake. Tilas ne dukkan ɓangarori su dakatar da buɗe wuta ba tare da ɓata okaci ba. Ci gaba da ruruta wutar rikicin zai jefa ɗaukacin yankin ne cikin hatsari.

Kafin sauka a Isra'ila gabannin lokacin da aka tsara tunda farko dai, Ban Ki Moon ya gana tare da shugaban ƙungiyar Larabawa Nabil al-Arabi a birnin alQahira na ƙasar Masar, wanda kuma ya ce har yanzu ba'a kaiga warware haƙiƙanin matsalar ba, wadda ya ce ba wai cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Gaza ba, amma kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila ke yi, matsayin da kuma shi ma kakakin ƙungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ke goyon baya:

Ya ce " Wanda ke mamaya da kuma wanda ya aikata kissar Jabari a lokacin da ake zaman lumana ne ya dace a ɗorawa alhakin rikicin dake afkuwa yanzu haka. Mun rasa shugabanni da mata da 'ya'yanmu, saboda haka ba za mu taɓa amincewa da duk wata yarjejeniyar da ba za ta bamu tabbaci ga tsaron lafiyar al'ummar Falasɗinu ba - ta kowane ɓangare."

Aƙalla makaman roka 60 ne Falasɗinawa suka harba kudancin Isra'ila a wannan Talatar kaɗai.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita        : Usman Shehu Usman 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani