A Hong Kong ana dakon tattaunawa
October 21, 2014Masu fafutukar rajin kafa dimokradiya a Hong Kong sun tsaya a tituna ana kallon-kallo da jami'an 'yan sanda gabannin fara tattataunawa da bangaren gwamnati da shugabannin masu fafutukar a ranar Talatan nan.
Babu dai labarin gwabzawa tasakanin masu fafutukar da 'yan sanda a yankin kasuwancin na Mong Kok a mashigar teku ta Kowloon, daya daga cikin manyan wurare uku da wannan zanga-zanga tafi kamari.
A yammacin jiya Litinin ne babbar kotun ta Hong Kong ta bada umarni ga masu zanga-zangar da su kauracewa dandalin da suka kafa a yankin na Mong Kok.
Tattaunawar dai da aka tsara a yau Talata tsakanin masu rajin dimokradiya da bangaren gwamnati, za a yada ta ne kai tsaye ta kafar talabijin inda za a tattauna kan batun tsare-tsare na zaben kasar.