1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A kalla mutane 200 ne suka rasu a Yemen

September 22, 2014

Sakamakon baya-bayan nan da hukumomin kiwon lafiyar kasar Yemen suka fitar, na cewa mutane 200 ne suka rasu yayin rikicin kasar, wasu kuma da dama sun ji rauni.

https://p.dw.com/p/1DH9l
Jemen Houthi-Rebellen
Hoto: REUTERS/K. Abdullah

Rahotanni daga Sanaa babban birnin kasar Yemen na cewa mutane 200 suka rasa rayukansu sakamakon fafatawar baya-bayan nan tsakanin 'yan tawaye 'yan Shi'a, da mayaka 'yan Sunni masu goyon bayan Jam'iyar Al-Islah da ke samun goyon bayan sojojin kasar.

Ofishin ministan kiwon lafiyar kasar ne ya sanar da wannan labari, inda ya kara da cewa, a yau ma dai jami'an agaji na wannan kasa sun karbi gawawaki 53, abin da ya kai adadin ga mutane 200 da suka rasu tun daga ran 16 ga watan nan na Satumba. Shugaban hukumar agajin kasar Docta Ali Saria, ya sanar cewa ma'aikatan nasu, sun dauki nauyin a kalla mutane 461 da suka samu raunuka a unguwar da ke arewa, dama arewa maso yammacin birnin na Sanaa sakamakon fadan.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Suleiman Babayo