1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Kwango an kashe maciji amma ba a sare kansa ba

November 8, 2013

Al'amura da dama su ka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako game da nahiyar Afirka da suka hada da halin da ake ciki a Mozambik da Niger

https://p.dw.com/p/1ADyH
Hoto: picture alliance/AP Photo

Yan tawayen Kwango na M23 sun sanar da cewar suna neman sulhu tare da gwamnati. Yayin da jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi da cewar an kashe maciji ne amma ba a sare kansa ba, wato ko da shike yan tawayen na M23 sun mika wuya, amma ba za a ce zaman lafiya ya samu kenan a kasar ta Kwango ba, ita kuwa jaridar Tageszeitung tambaya tayi: shin bayan nasarar sojojin gwamnati, yanzu kuma sai ina? Me zai biyo bayan kungiyar M23?

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi a game da matakan da gwamnatin Jamhuriyar Niger ta dauka, bayan da aka gano gawarwakin mutane masu yawa da suka mutu, sakamakon kishirwa a hamadar arewacin kasar, kan hanyar su ta neman shiga Aljeriya. Jami'an tsaron kasar ta Niger sun kara tsananta bincke da sintiri a iyakokin kasar na arewa, inda ma a farkon wannan wata suka tsare mutane kimanin 150 cikin wasu motoci biyar dake kan hanyar shiga Aljeriya. Tun bayan da aka gano gawarwakin mutane 92 a arewacin kasar a kusan karshen watan jiya, gwamnatin ta Niger tace zata dauki tsauraran matakai kan yan gudun hijiran dake maida kasar wurin wucewarsu zuwa Turai ko Afirka ta arewa. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace mafi yawan masu amfani da Niger domin wucewa zuwa Turai ko Aljeriya, sukan fito ne daga kasashe makwabta, kamar Najeriya ko Benin ko Togo ko Ghana ko kuma Cote d'Ivoire, ko kuma su kansu yan Niger dake neman fita ketare domin farautar abin duniya.

Kasar Mozambik tana fuskantar barazanar sake tsunduma cikin wani sabon rikici na cikin gida. Wannan dai shine abin da jaridar Neues Deutschland tayi sharhi kansa a wannan mako, inda ta nunar da cewar tsohuwar kungiyar nan ta yan sari ka noke, wato RENAMO tace ta soke yarjejeniyar zaman lafiya dake tsakaninta da gwamnati, kuma zata koma ga yakin da kasar ta dakatar a shekaru na tamanin. Sai dai kuma jaridar tace RENAMO da alamu tana gagwarmayar neman kada ta bace ne gaba daya, tana kuma neman ita ma ta shiga a dama da ita a bunkasar tattalin arzikin da Mozambique take samu yanzu. Kungiyar ta dauki makamai ne a shekara ta 1975, lokacin da Mozambique ta sami mulkin kanta daga hannun Portugal, kuma jam'iyar FRELIMO ta karbi aiyukan mulki.

Mosambik Krise Präsident Armando Guebuza mit Soldaten 24.10.2013
Shugaban Mozambik Armando Guebuza tare da sojojinsaHoto: Ferhat Momade/AFP/Getty Images

A karshe, jaridar Neue Zürcher Zeitung tayi nazari a game da hangen makomar tattalin arzikin kasashen Afrika. Jaridar tace shekara da shekaru kamfanoni da kasashe masu arziki suna zuba dimbin jari a nahiyar Afirka da suke ganinta a matsayin nahiya mai bunkasa, to sai dai hakan abu ne dake tattare da hadarori. Hukumar kudi ta duniya IMF, a wani rahoto kan tattalin arziki Afirka da ta gabatar a Lagos a makon jiya, tace kasashen Afika a yanzu sun fi kasancewa cikin hadari, sakamakon fadi-tashin al'amuran kudi a uniya fiye da ko wane lokaci can baya, saboda duk wata matsala da zata sami kasashen masu arziki, zata tsallaka zuwa ga kasashen na Afirka.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh