1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Jaruman fina-finan Hausa na samun karbuwa sosai

Zulaiha Abubakar MNA
August 5, 2019

Sana’ar fina-finan Hausa da wakoki na daga cikin sana'o'in da masu yinsu ke kirga riba, farin jinin jaruman fim ya sanya sun samu karbuwa tsakanin mata da maza musamman ma matasa.

https://p.dw.com/p/3NMiC

Jihar Kaduna guda ce cikin jihohin da jaruman wasan fim da mawaka suke zaune don gudanar da sana'o'insu na debe wa jama’a kewa da kuma ilmantarwa, lamarin da ya sanya duk macen da tsananin shukin son ganin jaruma ya kamata sai ta tattaro kayanta ta zo ta yi ta ragaita, idan an yi sa'a wasu su dace har su shiga sana'ar a fara damawa da su.

Yanzu haka dai sana’ar fina-finan na Hausa da wakoki na daga cikin sana'o'in da masu yinsu ke kirga riba, farin jinin jaruman fim ya sanya sun samu karbuwa tsakanin mata da maza musamman ma matasa.