1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Kalubalen mata a wasan kwallon kafa

Binta Aliyu Zurmi MNA
July 29, 2019

Shirin na wannan mako zai tabo irin kalubalen da mata masu wasan kwallon kafa musamman a arewacin Najeriya ke fuskanta tsakanin al'umma duk kuwa da irin amfanin da ake samu a wasan kwallon kafar a duniya.

https://p.dw.com/p/3Mtn1

Duk da kalubalen da mata ke fuskanta a wasan kwallon kafa, a wasu lokutan ma har da kyama, da dama daga cikin mata masu wasan kallon kafa sun  ce bakin rai bakin fama.

Ana yi wa wannan sana'a ta kwallon kafa kamar abu mai wahala musamman a arewacin Najeriya.
   
A wasu lokutan ma ana danganta matan da suka zabi sana'ar wasan kwallon kafa da dabi'un da suka danganci rashin kamun kai. Sai dai sun ce ba dukka aka taru aka zama daya ba, hasali ma a cikin kowacce sana'a ana samun bata gari.